Kotu ta dage ranar yanke hukunci kan kasurgumin dan damfarar nan dan Najeriya mai tashe a kafafen sada zumunta, Ramon Abbass wanda aka fi sani da Hushpuppi kan damfarar mutane miliyoyin daloli a kasashe daban-daban.
Kotun da ke zamanta a yankin California na kasar Amurka ta dage zaman yanke hukuncin ne zuwa 11 ga watan Yuli, 2022, sabanin ranar ranar Juma’a 14 watan Fabarirun da aka sanya da farko.
- ’Yar kasar Faransa mai shekara 14 ta haddace Alkur’ani cikin wata 4 a Zariya
- Lauyoyin Abduljabbar na neman a dawo da shaidar gwamnati na farko don su yi masa tambayoyi
Sanarwar da kotun ta fitar ranar 2 ga Fabrairu, 2022, ta ce, “Bisa bukatar lauyoyi, an dage ranar yanke hukuncin zuwa ranar 11 ga watan Yuli, 2022, da misalin karfe 11:00 na safe.”
Tun da farko kotun ta sanya ranar yanke hukunci ne bayan wanda ake zargin ya amsa a gabanta cewa ya damfari mutane na miliyoyin daloli a kasashe daban-daban na tsawon shekaru.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Otis D. Wright, ya kuma ba da umarnin a ci gaba da tsare Hushpuppi wanda ke fuskantar zargin damfarar mutane miliyoyin daloli a sassan duniya.
Sanarwar kotun ta bayyana cewa alkalin ya dage zaman ne bisa bukatar lauyoyin da ke kare Hushpuppi karkashin jagorancin Louis Shapiro.