✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuncin zinar hannu

Assalamu alaikum wa rahamatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan batutuwan da za su zo cikinsa, amin.Wannan…

Assalamu alaikum wa rahamatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan batutuwan da za su zo cikinsa, amin.
Wannan fili ya samu sakonnin tes da yawa daga ‘yan uwa matasa masu fama da muguwar dabi’ar nan ta zinar hannu, suna neman yadda za su rabu da wannan kazamar dabi’a. Ga bayani kan hukuncin zinar hannu da hanyoyin da matashi zai bi don rabuwa da wannan muguwar dabi’ar, da fatan Allah Ya sa a dace, amin.
Ma’ana: Zinar hannu na faruwa ne lokacin da matashi ya yi amfani da hannuwansa wajen sarrafa al’aurarsa, sannan ya tsundumar da kansa cikin tunane-tunane na alfasha da haka har ya kai ga biyan bukatar sha’awa.
Hukuncin zinar hannu a shari’a
In aka dubi nassin Al’kurani Mai Girma da Hadisan Manzon Allah SAW, za a fahimci cewa, zinar hannu hukuncinsu daya da zinar asali, watau dukansu haramun ne.
Domin tun farko, Allah Madaukakin Sarki hani ya yi ga kusantar zina gaba dayanta:“Kuma kada ku kusanci zina, Lallai ita ta kasance alfasha kuma hanya mummuna (Wadda za ta kai mutum ga halaka).” 17:33
“Kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha, abin da ya bayyana gare ta da abin da ya boyu”6:151
Daga wadannan ayoyi masu albarka, muna iya fahimtar cewa ya zama wajibi ga Musulmi a kodayaushe ya nesanta kansa daga duk wani abu da zai kusantar da motsuwar sha’awa irin ta zina gare shi, irinsu kallo ko tunani da zai motsar da sha’awa, ko kadaita da macen da ba muharrama ba.
Haka kuma da Yake jero kyawawan dabi’un Mu’munai, Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana cewa Mumunai su ne: “Wadanda suke ga farjojinsu masu tsarewa ne, Face a kan matan aurensu ko abin da hannuwansu na dama suka mallaka, to in su kai haka sun kubuta daga laifi. Amma duk wanda ya nemi wani abu bayan wannan, to wadannan su ne masu ketare haddi.”k: S23:A5-7
Don haka zinar mutum daya na daya daga cikin neman wani abu bayan wanda Allah Ya yarda da shi, bayan wanda yake halal.
Da yawa masu wannan dabia na fakewa da suna yi ne don tsoron kada su fada ga zina: wannan ba komai ba ne illa hudubar shaydan a gar eku; domin indai har tsananin jin yunwa bai sa mutum ya ci kashinsa ba, to bai ko dace ba tsananin sha’awa ya sa a yi zinar hannu ba, domin zinar hannu da ta zinar asali duk sunansu zina dai, don haka ya zama wajibi gare ku ku yi kokarin guje wa zinar hannu kamar yadda kuke kokarin guje wa zinar asali.
Illolin zinar hannu
1.    Ku sani ya ku matasa da suka dabi’antu da wannan dabi’a, bayan luwadi, alfasha mafi girma ita ce zina; a ayoyi da dama cikin Al-kur’ani mai Girma, Allah SWT Ya kwatanta girman zunubin zina da na shirka da kisan kai:
 “Kuma wadanda ba su kiran wani Ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki, kuma ba su yin zina, kuma wanda ya aikata haka (watau zina), zai gamu da sakamakon laifukansa: A rubanya masa azaba a ranar kiyama kuma ya tabbata  a cikinta yana wulakantacce.” k. S25; A68.
To yanzu wa zai so  kasancewa cikin masu irin wannan laifin? Da fatan Allah Ya tsare mu duka, amin.
2.    Hadisin Manzon Allah SAW ya nuna mai yin zinar hannu yana cikin tsinuwar Ubangiji Madaukaki; yana daga cikin mutane bakwai da Allah ba zai Kalle su ba, ba zai tsarkake su ba, kuma za su shiga cikin wutar jahannama; sannan  za a tashe shi da katon ciki na haihuwa a hannunsa.
3.    Haka kuma yana daga cikin illolin wannan dabi’a lahanta gabobin ibadar aure, ta yadda bayan an yi aure ba a iya gamsar da iyali saboda an riga an saba cim ma biyan bukata cikin sauri.
4.    Binciken masana kimiyya ya nuna yawan yin zinar hannu na haifar da sudewar gashin kai (sanko), domin yana sa yawaitar sinadarin sha’awa (testosterone) cikin jini, in ya yi yawa kuma jiki na sarrafa shi zuwa ga wani sinadarin (DHT) wanda shi ke haifar da sudewar gashi.
Mu sani, duk abin da Allah Ya yi umarni da shi, to abin nan za ka tarar mai tsananin alfanu ne ga rayuwar bil Adama, kuma duk abin da ya yi hani da shi, to abin nan mai cutarwa ne ga rayuwar bil Adama. Dubi irin girman illolin zinar hannu a duniya da lahirar mai aikatawa, don haka yana da matukar muhimmancin ga duk wani dan uwa matashi (ko ma ba matashi ba) mai aikata irin wannan kazamar dabi’a, ya yi niyyar rabuwa da ita ya kuma inganta niyyarsa, ya kasance zai yi hakan ne domin tsoron Allah da neman yardarSa kadai ba don wani abu ba.
Kada matashi ya ce to in ya daina, ya zai yi da tsananin sha’awarsa? Ko ya ce sai ya yi aure zai daina, ba a jinginar da tuba domin ba wanda ya san ranar mutuwarsa; yi la’akari da dimbin illolin da wannan dabi’a za ta haifar wa rayuwar duniyarka da lahirarka, wannan zai taimaka da kara maka himmar ganin ka rabu da ita; da fatan Allah Ya ba da ikon dagewa, amin.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba inda bayani zai zo kan matakan rabuwa da zinar hannu, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.