Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bukaci masu hada-hadar manhajojin na’urorin kwamfuta a kasar nan su yi rajista da hukumomin gwamnati da suka dace su karbi lasisin tafiyar da hada-hadar kasuwancinsu.
An bukaci gamayyar masu hada-hadar manhajojin na’urorin kwamfuta a karkashin Kungiyar Masu Gyaran Wayoyin Salula da Manhajoji ta Najeriya (AHHSRON) su yi rajista da hukumomin gwamnatin da suka dace ne don tsara kasuwancinsu ta yadda za su kasance cikin masu ruwa-da- tsaki a harkokin tarho.
Hukumar ta sanar da haka ne a wata sanarwa a ranar Juma’ar makon jiya inda ta ce hakan ya biyo bayan wani bincike da ofishin shiyya ya yi wanda ya gano kasancewar kungiyar a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan.
Ta bayyana cewa ofishin shiyyar na Hukumar NCC ya gayyaci shugabannin kungiyar zuwa taro don tattauna yadda za su hada gwiwa don tafiyar da bangaren tarho.
Kwanturolan Shiyyar Ibadan na Hukumar NCC, Yomi Arowosafe ya shaida wa mambobin kungiyar cewa tattaunawar ta zama wajibi saboda yadda hukumar ke son tattabar da sanya ido. Ya bayyana cewa hakan na bukatar sanya tsari da dokoki da kuma sanya ido sosai.
A taron wanda ya gudana a garin Ibadan, Arowosafe ya fada wa mambobin kungiyar muhimman ayyuka da nauyi da aka dora wa hukumar da kuma ikon da take da shi tare da yin amfani da taron wajen ilimantar da su kan tsara kasuwancinsu tare da samun lasisi.
Da yake jawabi, Shugaban Kungiyar, Edowaye Eboigbe ya ce kungiyar tana da mambobi fiye da dubu shida a Jihar Oyo inda ya bayyana kalubalen da kungiyar take fuskanta wanda ya ce ya hada da yawan kame da musguna wa mambobinsu da ’yan sanda ke yi a jihar.
Arowosafe ya bayyana bukatar mambobin kungiyar ta sanya kasuwancinsu cikin tsari da karbar lasisi yadda za su gudanar da harkokinsu kamar yadda doka ta tanada don kauce wa kame da musgunawa. Ya shawarci shugabannin kungiyar su tabbatar da sun san abubuwa da hukumar ta amince da su da kuma dokar harkar kayayyakin kimiyyar sadarwa.
A wata sabuwa kuma Hukumar NCC ta ce ta himmatu wajen kare sararin samaniyar sadarwa ta kasa kuma tuni ta fitar da tsarin ka’idojin gudanar da masana’antar Intanet da yadda za a gudanar da ita ga masu hada-hadarta.
Mataimakin Daraktan Harkokin Abokan Hulda na Hukumar NCC, Malam Ismaila Adedigba ya bayyana haka a ranar Alhamis a garin Benin a taron abokan hulda karo na 106. Adedigba ya ce tsarin Intanet wani yunkuri ne na kare yanar gizon kasar nan daga duk wata barazana daga ’yan dandatsa.
“Tsarin zai magance abubuwa kamar kare ’yancin yara ta yanar gizo da ’yanci da kare data da sauransu. Yayin da shiga wasu tsare-tsare na shiga tsakani ke kan hanya don tsabtace hada-hadar Intanet da masu amfani da tarho ya zama wajibi su bayar da gudunmawarsu ta hanyar daukar kamfe din Hukumar NCC da muhimmanci.
Adedigba wanda ya bayyana cewa bukatar amfani da yanar gizo tana karuwa ya kara da cewa Hukumar NCC ta tsara shirye-shirye don rage tasirin laifukan yanar gizo kan abokanen huldar tarho a Najeriya.
A gabatarwarsa wani kwararre, Mista Abdulazeez Jide ya bukaci masu amfani da tarho su kare kansu ta hanyar boye kalmarsu ta sirri tare da sauya ta a kai-a kai. “Kada ka maimaita kalmarka ta sirri a Intanet ka tabbatar ka yi amfani da kalmar sirri mai karfi tare da canja ta a kai-a kai,” inji shi.
Ya ce taron ilimantar da abokan hulda ya kamata Hukumar NCC ta ci gaba da yinsa.
Gwamna Godwin Obaseki wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa, Paul Ohunbamu ya yaba wa Hukumar NCC kan tsarin da ta bullo da shi. Ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin a shirye take wajen tabbatar da kare ’yancin jama’a.
Ya ce “Shirin zai bai wa mutane dama su gabatar da korafinsu tare da tattauna yadda za a dakile laifuffukan da ake aiwatarwa a Intanet.”