✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hukumar kwastam ta kama tulin harsasai a Oyo

An boye makaman da aka yi fasakwaurinsu a garin amala.

Jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya sun kama makamai da aka yi fasakwarinsu a cikin garin amala a Jihar Oyo.

Rundunar Kwasatam ta FOU shiyyar Zone A ta ce ta kama makaman ne a wani samamen ba-zata da jami’anta suka kai a yankin Iseyin na jihar ta Oyo.

Kwanturola mai kula da shiyyar, Kehinde Ejibunu, ya ce a halin yanzu tana kokarin kamo masu hannu a fasakwarin miyagun makaman da aka kama.

Kehinde Ejibunu, ya ce mai motar da ta dauko makaman ya cika bujensa da iska bayan ya hango jami’an hukumar.