Daga shafi na 26
Aminiya: Me za ka ce ga wadanda za su ce idan dokar ta tabbata za ta fi aiki kan talakawa ne kawai?
Wannan kyakkyawar tambaya ce kuma wannan maganar gaskiya ce. Amma abun da nake so na sanar da kai shi ne, kamar yadda na ce, idan abubuwa sun rikice akan bullo da wadansu tsari. Hukumar nan da ake neman a yi da kotun nan da muke neman a kafa, idan ka lura da abun da jihar Kano ta yi, ta je ta zabo malamai ne wadanda bisa tarihinsu kowa ya sannsu malamai ne masu ilimi da tsoron Allah, kuma ba sa jin tsoron fada wa duk wanda ya keta haddin addinin Musulunci gaskiya. Irin wadannan mutanen muke son dokokin da za a yi su yi tanadi da su. Ba wai alkalai za a je a dauko ba. A’a malamai za a nema, an sansu, irin wadanda ba sa fadanci ga kowa, za su iya fada wa mutane gaskiya, kuma an san cewa su Allah kawai suke tsoro. Malamai ne da dokokin addinin Musulunci suke tsaro, kuma za su yi iyakacin kokarinsu don tsara a kan haka. Wannan shi ya sa ake ganin za a samu canji daga abubuwan da aka saba da su. Na cewa kasar nan da an yi doka a kan talaka take aiki, ba ta aiki a kan mai hali ko basarake. Insha Allahu za a samu kyakkyawan canji a kan wannan al’amari.
Aminiya: Me za ka ce ga wadansu da ke ganin cewa yadda aure yake da sauki a kasar Hausa ne dalilin da ke taimakawa wajen yawan mace-macensa?
Wannan gaskiya ne. Saboda da ma shi addinin Musulunci bai tsaurara ba wajen maganar aure kuma saboda ana so ne ita yarinyar ta samu miji a kan lokaci. Addinin Musulunci bai tsaurara hanyar da za a bi a yi aure ba, amma ya tsaurara wajen maganar saki. Matsalar ita ce ka’idojin da addinin Musulunci ya shinfida game da saki, ba a binsu kuma ita ce babbar matsala. Domin idan ana binsu, sakin na da wahala ya faru. Daga dukkan abubuwan da Allah ya halasta, ba abun da ba ya so idan ba saki ba. Saboda haka kamar yadda na fada a zauren Taron kasa, cewa sharuddan addinin Musulunci game da sakin mace kamar tanadin tsarin mulkin Najeriya ne game da kirkiro jihohi, wanda abu ne da kusan da za ka ce ba ya yiwuwa. To wannan muke so a tabbatar da shi. Idan mutum ya san matarsa ba za ta saku ba. Idan kuma ba ya da halin kara auren, ko muhallin aje ta, to maganar ya kara aure ba ta ma taso ba. Saboda idan muka bi duk ka’idojin nan na saki, muna ganin za su rage mana wadannan matsaloli.
Aminiya: Wane karin bayani za ka yi game da masu fakewa da hadisin nan na Manzon Allah (SAW) wajen kara aure ba bisa ka’ida ba?
Malamai na addinin Musulunci ya kamata da su yi wa jama’a kyakkyawan ko cikakken bayani game da wannan hadisi. Cewar Manzon Allah (SAW) ya ce,ku yi aure, ku hayayyafa don ya yi alfahari da mu ranar Tashin Alkiyama, ai yana nufin sai kana da halin da za ka yi auren da yawa kafin ka yi. Ba wai kawai yana nufin abun da za ka ci da ita ba. A’a yana nufin har da tarbiyyar da za ka ba ’ya’yan da za ku haifa. Kana zaton Manzon Allah zai yi alfahari da danka wanda yake mashayi, ko wanda ya mutu a kan fashi da makami, ko a kan wata mummunar dabi’a. Yaya Manzon zai yi alfahari da shi a ranar Tashin Alkiyama? Saboda haka malamai na addinin Musulunci suke da hakkin yi wa mutane cikakken bayani game da abun da wannan hadisi ke nufi. Ba ma wai laifin malamai ne kawai ba, su kansu mutanen suna da nasu. Domin kawai mutum na son ya kara mata sai ya zo maka da wannan hadisin. Ya auri mata ya kuma kasance sau daya kawai yake ba ta abinci a yini. Ita za ta je ta yi aikin kwadago, ko ta je aikace-aikace a gidajen masu hali. Tana ci da kanta, tana ci da diyarta. Wannan daukan alhaki ne kuma daukar zunubi ne. Idan kana da hali kana iya yin mata hudu, amma sai idan za ka kula da su da abinci da lafiya da tarbiyya da makaratu da kuma magani. Ya kamata ’ya’yanka su yi karatun addini da na zamani, wanda shi ne na koyan sana’o’i. Amma Allah bai dora wa gwamnati wannan nauyin ba. Addinin Musulunci kai ne ya aza wa wannan nauyin na ilmantarwa da tarbiyya da kulawa da sauransu. Yakamata mutane su fahimci wannan. Wannan hujjar da mutane ke kafawa ba hujja ba ce. Kuma idan mutane suka dogaro a kan ta, ranar Tashin Alkiyama za su gane kurensu.
Aminiya: Wane kokari kake yi na ganin wannan bukata taka ta tabbata, musamman a jihohin arewacin kasar nan inda Musulmi suka fi rinjaye?
Dangane da wannan na fara magana da Mai Shari’a Bilkisu Aliyu. Inda ta ce dukkanin matar da ke zauren Taron kasa daga jihohin Arewa sun ce ta karbo wannan batun da na gabatar, ta rubuta shi a cikin harshen shari’a domin za su yi kungiya a je a gabatar wa kowane gwamna kuma za su bi diddigin ganin cewa gwamnonin Arewa sun yi amfani da wannan shawarar. Matan ba sa son a jira sai Gwamnatin Tarayya ta dauki wani matsayi game da wannan al’amari. To ba ma wai matan kawai ba, mu kanmu maza da ke wannan zauren taro daga yankin arewacin kasar nan, batun na cikin abubuwan da idan mun gama wannan taron, za mu samu gwamnoni da sarakuna na jihohinmu don sanar da su shawarwarinmu da kuma irin auren da ya kamata mu sake daurawa, idan muna so mu shiga cikin sahun gaba wajen gudanar da al’amuran kasar nan.
….hukuma da kotun da za su yaki sakin mata barkatai
Daga shafi na 26Aminiya: Me za ka ce ga wadanda za su ce idan dokar ta tabbata za ta fi aiki kan talakawa ne kawai?…