Wani dan Najeriya kuma mazauni a kasar Amurka mai suna Prince Denis Abuda, ya rasa ransa yayin da masu garkuwa da shi suka kashe bayan karbe kudin fansa daga wajen ‘yan uwansa a Jihar Edo.
‘Yan bindigar sun yi garkuwa da shi tare da wasu yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Legas domin koma wa kasar Amurka.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji a Edo
- An yi garkuwa da shugaban ma’aikatan jihar Edo
- An cafke masu satar mutane biyu bayan kashe yaran da suka yi garkuwa da su
- An yi garkuwa da mutum 50 a Neja
Abudu wanda shi ne shugaban cibiyar ‘Amerika-Furga’ ya dawo Najeriya ne don yin hutu, inda ya fada tarkon masu garkuwa da mutane a kan hanyar Benin zuwa Legas.
Iyalansa sun gano an yi garkuwa da shi ne bayan sun shafe awanni suna jiransa a filin tashin jirage na jihar Legas, inda wadanda suka yi garkuwa da shi suka sai sun biya fansar Naira miliyan 10 kafin su sake shi.
Rahotanni sun bayyana cewa da misalin karfe 7 na daren ranar Talata masu garkuwar suka sako ragowar mutanen da suka sace tare da Abudu.
Ragowar mutane da aka sako sun shaida wa iyalan Abudu cewar ‘yan bindigar sun kashe shi yayin da suka sako su, saboda gudun kada ya tona musu asiri.
A yammacin ranar Talata ne iyalan Abudu suka samu gawarsa kwance inda masu garkuwa suka kashe shi.
Neman jin ta bakin Kakakin ‘yan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwanburzor, ya ci tura a yayin da bai daga waya ballanta a samu tabbacin faruwar lamarin.