✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Hotuna: Gwagwarmayar maza don tsira da mutunci

Kayatattun hotuna da suka yi zarra a Gasar Daukar Hoto ta Aminiya na watan Nuwamba, 2021.

Ga kayatattun hotuna biyar da suka ciri tuta a Gasar Daukar Hoto ta Aminiya ta watan Nuwamban 2021.

Alkalan gasar sun zabo hotunan da suka yi zarrar ne daga cikin wadanda dimbin mutane da suka shiga gasar da aka tsara domin ba wa mutane damar bayyana fasaharsu ta daukar hoto.

Taken gasar ta wannan karo shi ne Gwagwarmayar Rayuwar Mazan Najeriya; A kowane wata za a sanar da batun da gasar za ta mayar da hankali a kansa.

Karo na farko ke nan da kamfanin Media Trust masu wallafa Aminiya da Daily Trust suka fara gasar daukar hoto na wata-wata.

Wani mai gyaran takalmi yana taka da aikinsa a kan layin Edward Ujege da ke birnin Makurdi, Jihar Binuwai. (Hoto: Aluga Luper Michael).
Wani mutum yana tura kura makare da robobi a hanyar Damboa da ke Maiduguri, Jihar Borno. (Hoto: Muhammad Abubakar Umar).
Wani saurayi yana wanke wata tukunyar abinci a gefen hanya. (Hoto: Usman Muhammad).
Wani makeri ya baje kwarewarsa a wurin wani bajekoli a garin Lakwaja, Jihar Kogi. (Hoto: Yahaya MK Ahmed).
Wasu masu sayar da soyayyen kifi a Kasuwar Kifi ta Bakin Cross a Karamar Hukumar Bade ta Jihar Yobe. (Hoto: Hussain Usman).