✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari a Daura

Atiku ya kai wa Buhari ziyarar ne domin girmamawa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a garin Daura da ke Jihar Katsina a ranar Asabar.

Mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin yaɗa labarai,  AbdulRasheed Shehu, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya kai ziyarar ne domin girmama Buhari.

Ziyarar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Atiku ya kai gaisuwar Sallah ga tsofaffin shugabannin ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) da Janar Abdusalami Abubakar a Jihar Neja.

Cikin waɗanda suka yi wa Atiku rakiya akwai tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Ga hotunan ziyarar a ƙasa: