✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Yahaya Bello ya miƙa wa Gwamna Ododo ragamar mulkin Kogi

Miƙa wa Ododo mulki ya kawo ƙarshen wa’adin Yahaya Bello na shekaru takwas.

Gwamna Usman Ahmed Ododo ya karbi ragamar mulkin Jihar Kogi, lamarin da ya kawo karshen wa’adin mulkin Yahaya Bello na shekaru takwas.

Dubban mazauna Jihar Kogi ne suka halarci bikin miƙa wa Ododo mulkin wanda aka gudanar a dandalin Muhammadu Buhari da ke Lokoja.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan Jihar Kogi, Kyaftin Idris Wada da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, na daga cikin mutanen da suka halarci bikin rantsuwar.

Ga wasu hotunan yadda bikin miƙa mulkin ya gudana:

Gwamna Ododo yana shan rantsuwar kama aiki
Gwamna Ododo matarsa yayin shan rantsuwar kama aiki
Gwamna Ododo bayan shan rantsuwar kama aiki
Yahaya Bello yana miƙa wa Gwamna Ododo mulki