Daruruwan mahaddata Al-Kur’ani sun yi dafifi a gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke unguwar Bompai a Kano don neman gurbin karatu da sabuwar cibiyar Nazarin Musulunci da ya kafa.
Matasa masu shekaru 15 zuwa 25 maza da mata daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano ne suka yi wa gidan nasa tsinke domin rubuta sunayensu gabanin tantancewar da za a yi kafin a fara karatu.
- An kama masu yunƙurin daura auren jinsi a Gombe
- Bayanan sahihancin takardun Tinubu sun yi karo da juna —Kotun Koli
A makon da ya gabata ne Kwankwanso ya kaddamar da Cbiyar Nazari da Bunkasa Musulunci ta Majidadi, domin magance matsalar gararambar almajirai masu shekaru 15 zuwa 25.
Cibiyar wadda ya ce wakafi ce ga mahaifinsa, za ta samar da ilimin Boko da na addinin Islama ga dalibai mahaddata Al-Kur’ani, wadanda za a tantance domin samun takardun na firamare, sakandare da kuma difloma.ertificates.
Kwankwaso ya bayyana cewa za a horas da daliban cibiyar a darussan Ingilishi da Laarbci wanda zai taimaka musu wajen tafiya daidai da zamani.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa akwai bangaran magidanta da cibiyar inda za a rika koyar da su a bangaren yaki da jahilci da kuma difloma a ilimin addinin Musulunci wanda da shi za su iya samun gurbin karatun jami’a.