Hotuna: Yadda dokar hana fita ta kasance a Plateau
Tun da karfe 12 na daren Alhamis ne dokar da gwamnatin jihar Filato ta kafa ta hana fita don kauce wa yaduwar cutar coronavirus ta fara…
Yadda wata unguwa ta kasance a cikin Jos
DagaHussaini Isah, Jos
Fri, 10 Apr 2020 18:07:04 GMT+0100
Tun da karfe 12 na daren Alhamis ne dokar da gwamnatin jihar Filato ta kafa ta hana fita don kauce wa yaduwar cutar coronavirus ta fara aiki.
Wakilin Aminiya ya zagaya wasu sassan Jos, babban birnin jihar don ganin yadda dokar ke tafiya.
Ga dai abin da ya gane wa idonsa:
Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong lokacin da yake kaddamar da shirin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a jihar
Ma’aikata na feshin maganin kashe kwayoyin cuta a cikin garin Jos babban birnin jihar Filato
Wasu ma’aikatan na shirin fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a cikin garin Jos, babban birnin jihar Filato.
Yadda wata unguwa a birnin Jos ta kasance fayau ranar juma’a bayan dokar hana fita ta fara aikiJami’an tsaro kawai ake iya gani a kan titi a wasu unguwannin Jos, babban birnin jihar filato