✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Yadda aka nada Ganduje da matarsa sarautar gargajiyar a jihar Delta

An gudanar da bikin nadin ne a ranar Asabar

Basaraken Urhobo da ke jihar Delta, Mai Martaba Ogbon, Ogoni, Oghoro na daya, Sarki Ohworode na daular Olomu, ya nada Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Farfesa Hafsat Umar Ganduje sarautar yankin.

Basaraken dai ya ba Gwamnan da matarsa sarautar Olorogun ne na masarautar ta Olomu.

An gudanar da bikin nadin ne fadar sarki Ohworode a gaban sauran masu rike da sarauta na masarautar, da manyan jami’an gwamnati na jihohin Delta da Kano, da ‘yan uwa da kuma dangin Gwamnan a ranar a Asabar.

Ga yadda bikin nadin ya gudana a cikin hotuna.

Isiowar Sarki Ohworode fadarsa gabannin soma bikin (Hoto: Meluwa Kelvin)
Gwamna Ganduje da matarsa tare da wasu masu rike sarautar gargajiya a fadar Sarkin gabannin soma bikin (Hoto: Meluwa Kelvin)
Sarki Ohworode fadarsa da gwamna Ganduje da matarsa da kum wasu daga cikin masu rike da sarautar gargajiya na masarautar gabannin soma bikin (Hoto: Meluwa Kelvin)
ISarki Ohworode na shirin nadin Ganduje sarautar a yayin bikin (Hoto: Meluwa Kelvin)
Sarki Ohworode na nadin Ganduje a da hular gargajiya a yayin bikin (Hoto: Meluwa Kelvin)
Sarki Ohworode na musabiha da Farfesa Hafsat Ganduje a cikin shirin ba ta sarautar gargajiya a cikin bikin (Hoto: Meluwa Kelvin)
Sarki Ohworode na sa wa Mai dakin gwamna Ganduje tsakiya da kuma hula a na sarautar gargajiya a cikin bikin (Hoto: Meluwa Kelvin)
Wasu daga cikin manyan bakin da su ka halarci taron bikin nadin a fadar Mai girma Ovie Dr. R. L Ogbon, Ogoni, Oghoro na 1. Rayal Canon, PhD+ OON, Sarki Ohworode na daular Olomu mai tsohon tarihi, (Hoto: Meluwa Kelvin)