✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: Ayyuka sun tsaya cak a Majalisa da NNPC bayan fara yajin aikin NLC

Tuni sauran kungiyoyi suka mara wa NLC da TUC baya wajen shiga yajin aikin.

Ayyuka sun tsaya a Majalisar Wakilai da hedikwatar Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) da ke Abuja a ranar Talata a sakamakon yajin aikin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka tsunduma.

Kungiyar kwadago ta umarci mambobinta a fadin Najeriya da su shiga yajin aikin don adawa da cin zarafin da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero, a Jihar Imo.

Duk da cewa Kotun Masana’antu ta Kasa (NIC) da ke Abuja ta hana kungiyoyin shiga yajin aikin, kungiyoyin sun uamrci mamboninsu da su tsayar da harkoki a duk wuraren aikinsu.

Ga hotunan yadda aka rufe Majalisar Wakilai da Hedikwatar NNPC:

Hedikwatar NNPC

 

 

%d bloggers like this: