Daya daga cikin ’yan matan da ’yan Boko Haram suka sace daga makarantar sakandiren Chibok a Jihar Borno a 2014, Joy Bishara, an yi mata baiko a kasar Amurka.
A watan Afrilun 2014 ne ’yan ta’addan suka sace ’yan matan su 276, galibinsu masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18, amma 57 daga cikinsu suka gudu ta hanyar dirowa daga motar da aka debe su.
- Za a kai ƙarar masu tunzara Ale Rufai mai Gangaliyon
- Hisbah ta cafke masu shirin daura auren jinsi a Kano
Daga bisani kuma sojojin Najeriya sun kubutar da da dama daga cikinsu, amma har yanzu akwai sama da guda 100 da suke hannun Boko Haram din.
To sai dai Bishara da wata ’yar uwarta, Lydia Pogu, wadanda suna daga cikin wadanda suka tsira daga harin a lokacin sun ja hankalin duniya bayan komawarsu Amurka.
Daga bisani ta kammala karatun digirinta a Jami’ar Southeastern, a shekara ta 2021.
Ga wasu hotunan baikon nata da saurayinta a kasar Amurka: