✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano

Duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

Wata gobara da ta auku safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.

Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri.

Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu ba su gano musabbabin tashin gobarar ba.