Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka fara a makon jiya cikin hotuna. Matasa sun yi zanga-zangar lumana kan yawaitar fyade a garin Gusau, Jihar ZamfaraFasinja na hawa jirgin farko bayan an bude filayen jirgi na cikin gida a Najeriya.Gwamnatin Tarayya ta janye bude makarantu ga dalibai masu kammala karatun firamare da kuma babba da karamar sakandareUban jam’iyyyar APC na kasa Bola Tinubu ya kai wa iyalan marigayi Abiola Ajimobi tsohon gwamnan Oyo, ziyarar ta’aziya.Majalisar dattawa soke duk abin da aka yi a shirin gwamnatin tarayya na daukar ma’aikata 774,000.Mohammed Umar ya zama mukaddashin shugaban hukumar EFCC mai yaki da almundahana.Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan sabon kasafin kudin shekarar 2020.Kasar Saudiyya ta dage ranar sa wa dakin Ka’abah farin kyalle zuwa ranar 1 ga watan Dhul Hajji.Shugaba Buhari ya dakatar da Ibrahim Magu daga jagorantar hukumar EFCC, sakamakon binciken sa kan zargin badakala.Allah Ya yi wa Alhaji Inuwa Abdulkadir, jigo a jam’iyyar PDP rasuwa.Gobara ta ci wani bangare na tashar wutar lantarki ta Danagundi a jihar Kano.Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sherrif ya kai ziyarar ba-zata a hedikwatar jam’iyyar APCYadda ake tantance fasinjoji bayan bude filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a ranar Asabar.Wani bene mai hawa uku ya rushe a lokacin da mazauna cikinsa ke barci da tsakar dare a jihar Legas.Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta yi wa ‘yan Najeriya alkawarin barin farashin mai a yadda ta rage shi zuwa N123 ba. Ga Share this:FacebookXLike this:Like Loading... Related