✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta lalata tirela 25 na giya, ta kama mutum 2,260 a 2022

Hukumar Hisbah ta ce za ta ci gaba da yaki da masu aikata munanan dabi'u a jihar.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta ce ta lalata tirela 25 na giya da kuma kama mutum 2,260 da suka aikata laifuka daban-daban daga watan Janairu zuwa Disamba a 2022.

Shugaban hukumar, Sheikh Harun Sani-Ibn ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Alhamis.

“Yawancin wadanda aka kama an mika su ga hukumomin da suka dace don daukar matakin da ya dace a kansu; masu kananan shekaru kuma an mika su ga iyayensu.

“Don rage barace-barace a cikin birni, mun kwashe mabarata 1,269, sannan mun mayar da 386 zuwa jihohinsu.

“Hukumar Hisbah ta yi nasarar tarwatsa tarukan badala 86 da sauran laifuka domin dakile munanan dabi’u a fadin jihar,” in ji shi.

Ibn-Sina ya ce hukumar ta sulhunta rigingimu sama da 822 a cikin shekarar, yayin da aka tura wasu zuwa kotu don warwarewa.

Ya kara da cewa Hisbah ta aurar da mutum 15, yayin da yi nasarar musuluntar da mutum 22.

Ibn-Sina ya ce gwamnatin jihar ta dauki ma’aikatan wucin gadi 5,700 aiki, tare da gyara gine-gine a hedikwatar Hisbah da kuma ma’aikatun kananan hukumominta.

Kwamandan, ya ce an kafa sabuwar kotun shari’a a hedikwatar hukumar, yayin da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya amince da daukaka masallacin Hisbah zuwa masallacin Juma’a.

Ya shawarci iyaye da su kara yin taka tsan-tsan tare da kai rahoton duk wanda ake zargi wajen aikata munanan dabi’u ga hukumomin da abin ya shafa.