Jami’an Hukumar Hisbah sun kama sama da katan 200 na barasa a babbar tashar motar Sakkwato.
A lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Laraba, Kwamandan Hisbah, Malam Usman Jatau ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa dokar Jihar Sakkwato wanda bai kamata mutane su rika saba dokar ba.
Ya ce ba wani zuwa yanzu da ya ɗauki alhakin shi ne mamallakin barasar, kan haka za su tuntubi Kwamishina Shari’a don sanin matakin da za a ɗauka na gaba.
Kwamanda Jatau ya ce, “tsare doka da oda ba ya na nufin musgunawa ko cin zarafin wani da kawo hargitsi da rashin zaman lafiya. Hukumar tana da dokoki da sharuɗɗan gudanar da aiki ga mutanen jiha.
- Fintiri ya rage ikon Lamiɗon Adamawa zuwa ƙananan hukumomi 3
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Albasa Tashin Gwauron Zabo
“Muna rokon jama’a su ji tsoron Allah a duk abin da suke yi, su guji saɓo a cikin lamurransu kamar cudanya a tsakanin mata da maza.
“Sanya sutura da gudanar da kasuwanci dole ne ya zama yadda addini ya shardanta.”
Ya ce “amfani da dama ta wuri da za ka iya ɓoyewa ka yi abin da bai dace ba haram ne, cin zarafi da cin amanar kowane Musulmi kai tsaye ko a kaikaice bai dace ba ga kowane Musulmi daga cikinmu.
“Dukkan bukukuwa da za a yi a jiha su zama daidai da karantarwar Shari’a, sayar da miyagun ƙwayoyi a cikin jama’a ko wurin taro kowane iri haram ne.”