✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hisbah ta kama karuwai da motar giya a Kano

Jami'an Hisbah sun cafke wata mota makare da kwalaben giya 8,600 a Jihar Kano.

Jami’an hukumar Hisbah sun cafke wata mota makare da kwalaben giya 8,600 a Jihar Kano.

Babban jami’in yaki kayan maye na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Idris Ibrahim, ya ce sun cafke motar ce a yankin Kwanar Dangora, bayan ta shigo daga Jihar Kaduna.

Ya ce tun tasowar motar daga  Kaduna suke lura da ita, tana shigar Jihar Kano kuma, “Muka tsare ta a Kwanar Dangora, direban ya yi yunkurin guduwa amma muka kama shi.

“Shan giya ko kasuwancinta laifi ne a Jihar Kano, don haka za mu gurfanar da direban a gaban kotu idan muka kammala bincike,” in ji shi.

Hisbah ta kama karuwai a Kano

Hakazalika hukumar ta kama wasu mata matasa 15 kan zargin su da karuwanci a sassan garin Kano.
Yankunan da Hisbah ta kai samame ta kama karuwai sun hada da Sabon Gari, Miyangu Road, Hadejia Road
Hotoro, Tinshama, Bakin River, da kuma Old Zoo Road Motor Park.

Aminiya ta gano cewa yawancin ’yan matan da aka kama ’yan shekaru 19 ne kuma ba karon farko da Hisbah ta kama su ba ke nan kan ayyukan badala.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano,
Mujahid Aminuddeen, ya ce yawancin ’yan matan an sha kama su har an gurfanar da su a kotu, amma har yanzu ba su daddara ba.

“Abin takaicin shi ne wasunsu daga wasu jihohi, wasu ma daga wasu ƙasashe suke zuwa nan suna karuwanci da sauran abubuwan badala.

“Saboda haka muke kira ga al’umma da su rika kawo mana rahoton duk inda suka ga irin wadannan abubuwa.

”Wasu daga cikin yaran kuma addu’a suke bukata, saboda idan aka zauna da su aka yi musu magana kan irin rayuwar da suke yi sai ka samu abin tausayi, wata wahala ce ta sa ta shiga harkar,” in ji shi.