Hukumar Hisba ta Kano na binciken wani malamin Islamiyya da ake zargi da yin lalata da daliban makarantar mahaifinsa da ya rasu a jihar.
Freedom Radio ta rawaito cewa kazantar lamarin ta kai ga har malamin Islamiyyar ya dirka wa guda daga cikin daliban nasa ciki.
- Kasashe 6 da suka fi iya Turanci a Afirka
- Wadanda suka rasu a girgizar kasar Turkiyya da Syria za su kai 20,000 —Jami’an lafiya
Makartanar Islamiyyar dai fitacciya ce a unguwar Nassarawa da ke Kano, kuma mallakin wani malami da yi fice wajen hidimta wa addinin Musulunci a jihar ne, wanda bayan rasuwarsa ’ya’yansa suka dauki gabarar koyarwa.
Majiyar tamu ta ce, bayan bullar cikin da malamin ya dirka wa guda daga cikin daliban nasa, ya aure ta; Inda suka hada kai da ita, tana jawo masa dalibai gidansu na aure, yana lalata da su.
Malamin Islamiyyar ya shiga hannun Hisba ne bayan an tsegunta mata yadda yake amfani da matsyinsa yana lalata da dalibansa mata.
Bayanai sun nuna wanda ake zargin yana nuna wa daliban cewa soyayya kawai yake son yi da su, idan suka amince kuma a hankali ya fito musu da bukatarsa.
Shugaban Hukumar Hisba Muhammad Harun Ibn Sina ya ce wata majiya ce ta tsegunta musu lamarin, kuma a binciken da suka fara gudanar wa sun gano akwai kamshin gaskiya a zarge-zargen.
“Mun fara bincike kan wannan batu, kuma mun gayyato shi wanda ake zargin mun masa tambayoyi kuma mun yi tattaki har makarantar ma don tattara bayananmu,” in ji shi.
Ya ce daga bayanan da suka tattara dai zai yi wuya a ce zargin ba gaskiya ba ne.