Tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Herry ya zama mai horar da kungiyar Monaco ta Faransa.
Herry mai shekara 41 a rayuwa, ya kasance mataimakin kocin kasar Belgium a gasar cin kofin duniya.
Ya fara wasan kwallo kafa ne da kungiyar Monaco kafin daga bisani ya koma Arsenal inda ya yi fice.
Herry zai maye gurbin Leornardo Jardim ne, wanda kungiyar ta sallama.