Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta ƙaru da kashi 33.88 a watan Oktoban 2024, adadin da ya nuna an samu ƙarin kashi 1.18 cikin ɗari daga kashi 32 cikin 100 da aka samu a watan Satumban 2024.
Hakan na ƙunshe cikin bayanan da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar a ranar Juma’a.
- Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC
- HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja
Alƙaluman sun nuna cewa an samu ƙaruwar hauhawar farashin sufuri da kuma kayayyakin masarufi a ƙasar.
“Alƙaluman hauhawar farashin kayan masarufi a watan Oktoban 2024 ya kai kaso 39.16 cikin 100, ƙarin kaso 7.64 cikin 100 kan adadin da aka samu a watan Oktoban 2023 (31.52%),” in ji NBS.
Hukumar ta ƙara da cewa an samu ƙari a farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da hatsi da kuma man girƙi, waɗanda suka kara yawan hauhawar farashin abinci da ake samu a kowane shekara.
Kazalika alƙaluman sun nuna yadda hauhawar farashin kayayyaki yake ta ƙaruwa a shekarar 2024.
A watan Yuni ma alƙaluman hauhawar farashin ya ƙaru zuwa kaso 34.19 cikin 100, adadin da ya zarce na watan Mayun na kashi 33.95 cikin 100.
Ana iya tuna cewa dai, jim kaɗan bayan hawansa kan mulki a watan Mayun bara, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kawo ƙarshen tallafin man fetur, wanda ya ce gwamnati ba za ta iya jure ci gaba da biya ba.
Wannan lamari ana ganin shi ne dalilin da ’yan Nijeriya ke fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin tabarbarewar tattalin arziki da aka taɓa gani a tsawon shekaru da dama, inda tsare-tsaren kuɗi a ƙasar suka sanya darajar Naira take ci gaba da faɗuwa idan aka kwatanta da dala.