Akalla mutum goma ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu mutum talatin suka samu munanan raunuka yayin da wani hatsari ya auku a tsakanin tireloli biyu da sanyin safiyar ranar Asabar a jihar Adamawa.
Mashaida wannan mugun gani sun labarta wa Aminiya cewa, tirelolin biyu da ke suke kan hanyar Mayobelwa zuwa Ganye, sun hadu junansu sakamakon gudun da ya wuce ka’ida inda daya ta nemi ta ketare daya.
- Mutum 9 sun mutu, 3 sun jikkata a hatsarin mota a Kano
- Hatsarin babbar mota ya lakume rayuka 2 a Anambra
Wasu daga cikin mutanen kauyen da suka ba da gudunmuwa wajen tattare gawarwakin mutum 10 da suka rasa rayukansu tare da kai dauki ga mutum 30 da suka jikkata, sun ce tirelolin biyu sun gwabza wa junansu a kauyen Jinmaa.
Jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) sun ba da tabbaci a kan wannan lamari da cewa hatsarin ya auku ne a sakamakon tukin gangaci da kuma gudun da ya wuce kima.
Sun ce an killace gawarwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya tare da mika wadanda suka raunata zuwa Asibitin Cottage da ke garin Mayobelwa.
“Mun hangi tireloli biyu suna tsula gudu yayin da suke kan hanya daya kuma kowacce tana kokarin ta wuce daya wanda a haka ne daya daga su ta kwace daga gudunarwar direbanta,” inji wani ganau.
“Yayin da muka kai dauki, mun riski fasinjojin da ke cikin tirelolin biyu suna ta kundunbala a kasa inda a nan wasu suka mutu take yayin da wasunsu sun samu karaya a hannuwa da kafafu.”
“Daya daga cikin wadanda suka mutu kansa ya rabu da gangar jikinsa.”