Wani hatsarin mota a ya yi sanadin mutuwar wata mata a kan babban titin Gbongan-Ibadan a Jihar Osun.
Hatsarin ya ritsa da wata mota ce kirar Toyota da kuma mota kirar Corolla.
- Najeriya ta rasa kwararren matukin jirgin ruwa a hadarin mota
- Shugaban Hukumar Aikin Hajji na Kaduna ya rasu a hadarin mota
- Mutum 22 sun kone a hadarin mota
- Tsohon Sakataren NUJ da mutum uku sun kone a hadarin mota
Jami’an ’yan sanda da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) sun kai agaji wajen tare ceto wasu daga cikin wanda hatsarin ya ritsa da su.
Yara uku da wani babban mutum guda daya sun samu raunuka kuma an garzaya da su zuwa asibiti.
Kakakin FRSC ta Jihar, Misis Agnes Ogungbemi, ta ce hatsarin ya auku ne sakamakon kwacewar mota kuma da an kimanta gudu ba za a samu salwantar rai ba.
Agnes Ogungbemi ta ce yara uku da karin mutum daya da suka ji rauni, motar agajin gaggawa ta ba su kulawa, sannan aka tafi da su asibiti.
Ta kara da cewa matar an dauke ta zuwa asibitin koyarwa na OAU da ke Ile-Ife, inda aka tabbatar da mutuwar ta.
Har wa yau, ta ce jakar hannu da katin cirar Kudi na ATM da kayan abinci da sauran abubuwan da aka samu a motar matar an damka su ga hannun ’yan sanda.