Akalla mutum 12 ne aka ba da rahoton rasuwarsu a wani hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Bida a Jihar Neja.
Hukumomi sun ce hatsarin ya auku ne lokacin da wata babbar mota da ke makare da waken soya da ridi da kuma mutane ta kwace daga kimanin nisan kilomita 12 daga Agaie.
- QATAR 2022: ‘FINAL’ Tsakanin Ajentina Da Faransa
- Maniyyata Kiristoci 300 daga Najeriya sun isa Jordan ziyarar ibada
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar, Kumar Tsukwam, shi ne ya tabbatar da hatsarin, inda ya ce ya auku ne da misalin karfe 5:00 na Asubar ranar Asabar, a kusa da Tsangayar Share Fagen Shiga Jami’ar IBB da ke Agaie.
Ya ce nan take mutum 12 suka rasu, wasu 10 kuma suka sami raunukua, kuma tuni aka garzaya da su Babban Asibitin Agaie, inda suke samun kulawar likitoci.
Kwamandan ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wasu manyan motoci da suka dauko kayan abinci daga Arewa, a kan hanyarsu ta zuwa Jihar Legas.
Ya alakanta hatsarin da gudun wuce sa’a da kuma koarin wuce abokin tafiya ba bisa ka’ida ba da kuma kin bin dokokin hanya a matsayin musabbabin hatsarin.
To sai dai mazauna garin na Agaie, sun ce daga cikin motocin ta kwace wa direbanta ne a kokarinta na kauce wa ramukan da ke kan hanyar, inda ta daki wata tankar mai da direbinta suka tsaya suna hutawa a gefen hanya.
Hatsarin na ranar Asabar daya ne daga cikin da dama da ake yawan samu a hanyar wacce ke cikin mawuyacin hali, inda suka ce ko a kwanakin baya wata tankar mai ta kwace ta kashe mutane masu yawa.