Wani hatsarin mota da ya auku a safiyar Talata a kudancin Pakistan ya yi sandiyar mutuwar mutum 20 tare da jikatar wasu mutum shida.
Lamarin ya faru ne sakamakon taho mu gama da wata tankar mai ta yi da wata motar bas a babban titin lardin Punjabi.
- Motar bas makare da ’yan sanda ta fada kogi a indiya
- Buhari ya nada Dangote ya jagoranci kwamitin dakile Maleriya a Najeriya
Bas din dai na makare da fasinjoji 24 da direbobi biyu, wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa garin Karachi daga Lahore.
’Yan Sanda dai sun ce direban tankar ya tsere bayan faruwar lamarin.
Sun kuma bayyana cewa sauran wadanda suka jikkata sakamakon kamawa da wuta da bas din ta yi, na kwance a asibitin Nishtar da ke birnin Multan domin karbar magani.
Dan sanda mai bincike kan lamarin, Kashif Shahzad, ya ce tuni dan sandan da ke bakin aiki lokacin da hadarin ya auku ya mika musu rahoto.
Ya kuma ce bayanan farko na nuna cewa tukin ganganci da direban bas din ke yi ne ya haifar da hatsarin, kuma direban na cikin wadanda suka rasu.
Tuni Fira-Ministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalin wadanda suka rasu a shafinsa na Twitter, in da ya ce ya na bakin ciki da asarar rayuka masu daraja 20 a hadarin.
shi ma dai babban Ministan Lardin Punjab Parvez Elahi ya bayyana bakin cikinsa tare da rokon jami’an da su ba da cikakken goyon baya ga iyalan mamatan da ke cikin damuwa.
Hatsarin mota dai a kasar ya zama ruwan dare, inda da yawa ke zargin manyan gine-gine da ake ba bisa ka’ida ba da hawa motocin da ba su dace ba, da kuma tukin ganganci ne ke haddasa shi.
Bayanai daga Ofishin Kididdiga na kasar na nuna cewa a shekarar 2021 kadai, an samu haduran mota sau 10,379 da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 4,566.