✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo

Motar ta murƙushe wata yarinya da ke tsaye kusa da kayayyakin mahaifiyarta, yayin da mahaifiyarta ta tsira da ƙyar,"

Wani direban motar bas ya murƙushe wata yarinya ’yar shekara biyu a ƙoƙarin gujewa kamun jami’an hukumar kare haƙƙin jama’a na Jihar Edo.

Lamarin ya faru ne a kan titin Ring Road da ke birnin Benin a ranar Laraba lokacin da jami’an hukumar suka yi artabu da wani direban motar bas a lokacin da suke ƙoƙarin kama shi.

Shaidu sun ce lamarin ya ta’azzara ne a lokacin da jami’an da ke aikin suka tunkari direban inda yake ƙoƙarin tserewa ya sauya hanyar motar, amma jami’an sun kama sitiyarin motar.

“Motar ta murƙushe wata yarinya da ke tsaye kusa da kayayyakin mahaifiyarta, yayin da mahaifiyarta ta tsira da ƙyar,” in ji wani ganau.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Edo, Moses Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an fara bincike.

“Wata farar motar bas ƙirar Vannette mai lamba BEN 406 YA ta afka kan masu tafiya a ƙasa a lokacin da take ƙoƙarin gujewa kamawar jami’an tsaron. Abin takaici, wata yarinya ’yar shekara biyu ta rasa ranta, yayin da mahaifiyarta ke jinya a asibiti a halin yanzu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, jami’in tsaron da ake zargi da haddasa haɗarin tare da direban a yanzu haka suna hannun ’yan sanda domin gudanar da bincike.