✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 4 a Kano

An ɗauki buhunan shinkafa biyu da babur ɗaya a cikin kwale-kwalen.

Mutum huɗu daga ƙauyen Kauran Mata na Ƙaramar Hukumar Madobi ta Jihar Kano sun riga mu gidan gaskiya yayin da kwale-kwalen da suke ciki ya yi haɗari.

Rahotanni sun bayyana cewa kwale-kwalen ya ɗauko mutum 16 a lokacin da ya kife ranar Talata da yamma.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wadanɗa haɗarin jirgin ya rutsa ke hanyar dawowa daga garin Ƙarfi na Ƙaramar Hukumar Kura inda suke aikin sarrafa shinkafar gida.

Kawo yanzu dai an yi nasarar ceto mutum biyar da ransu ciki har da direban kwale-kealen da wata mata mai goyo amma ɓa a ga ɗan da take goyon ba.

Har yanzu dai ana ci gaba da laluben sauran fasinjoji shida da hatsarin ya rutsa da su.

Jami’in hulɗa da jama’a na Ƙaramar Hukumar Madobi, Jamilu Mustapha Yakasai ya tabbatar da gano gawarwakin mutum huɗu.

Ya bayyana sunayensu mamatan da suka haɗa da Maryam Jibrin, Yusuf Galinja, Kabiru Muhammad da Safiyanu Musa, waɗanda ya ce an yi masu jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar.

Ya ce Kantoman Ƙaramar Hukumar Madobi, Alhaji Muhammad Sani Gora ya ziyarci ƙauyen Kauran Mata domin jajanta wa jama’a kan lamarin.

Wani mazaunin Kauran Mata, Salisu Adamu Baure ya ce wannan shi ne karo na farko da irin wannan mummunan hatsarin ya afku, inda ya alaƙanta shi da ɗaukar lodi fiye da kima.

Ya ce an ɗauki buhunan shinkafa biyu da babur ɗaya a cikin kwale-kwalen.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Kansilan Kauran Mata, Aminu Garba ya kai masu rahoto.