✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harry Kane ya koma Bayern Munich da taka leda

Na ji dadi matuka da na zama dan FC Bayern a yanzu.

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila, Harry Kane, ya koma Bayern Munich da taka leda bayan kulla yarjejeniyar shekaru hudu da kungiyar ta kasar Jamus.

Kane wanda ya raba gari da Tottenham ya rattaba hannu kan yarjejeniya da Munich har zuwa 2027, kamar yadda kungiyar mai buga gasar Bundesliga ta sanar a ranar Asabar.

Tottenham Hotspur ta sayar da tauraron nata mai shekaru 30 kan euro miliyan 100, kwatankwancin dala miliyan 110 ke nan.

“Na ji dadi matuka da na zama dan FC Bayern a yanzu,” kamar yadda Kane ya bayyana a sanarwar da kulob din ya fitar.

Zakarun na kasar Jamus na cikin matsananciyar damuwa inda suke ta neman dan wasan gaba, bayan sun sha gwagwarmayar cike gurbin Robert Lewandowski a kakar da ta gabata.

Kane ya ci kwallaye 280 a wasanni 435 da ya buga a Tottenham kuma shi ne ya fi kowa cin kwallaye a Ingila, inda ya ci kwallaye 58 a wasannin kasa da kasa.

Har yanzu dai bai ci kofi a wata babbar gasa ba a kulob dinsa ko kuma a matakin kasa.

Akwai yiwuwar Kane zai buga wasan karshe da Munich za ta buga da RB Leipzig a gasar German Super Cup a yau Asabar.