✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu son mu yi wa Tinubu juyin mulki za su ji kunya —Sojoji

Rundunar Tsaron Najeriya ta yi zargin cewa wasu marasa kishi na neman zuga ta ta yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.

Rundunar Tsaron Najeriya ta yi zargin cewa wasu na neman zuga ta domin yi wa gwamnatin zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu juyin mulki, amma ba za ta ba da kai bori ya hau ba. 

Kakakin Hedikwatar Tsaron Najeriya, Birgediya Tukur Gusau ne ya bayyana hakan a saƙon da ya aiko wa wakilinmu a safiyar Asabar, inda ya bayyana masu ƙulle-ƙullen da cewa “miyagu marasa kishin ƙasa” ne.

Amma Janar Tukur Gusau bai yi ƙarin haske game da waɗanda yake zargin suna neman hure wa sojojin kunne ba.

“Wannan wani kinibibi ne da neman kawar da hankalin sojoji daga ainihin aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu,” in ji shi.

Ya jaddada ce duk irin zuga da za a yi musu, sojoji ba za su taɓa yin abin da zai kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya da aka samu da jiɓin goshi ba.

Birgediya Tukur Gusau ya kara da cewa, maimakon sauraron masu mugun nufi na neman juyin mulki, sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da aikinsu na kare ƙasa, kuma ba za su saurari masu neman hana ruwan Najeriya gudu ba.

Gusau ya yi wannan martani ne bayan wasu kiraye-kirayen da ke neman sojoji su karɓe mulki, saboda zargin gwamnatocin ’yan siyasa da kasa magance matsalolin ƙasar.

Amma Birgediya Gusau, ya jaddada cewa Rundunar Tsaron Najeriya ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsanta, Janar Christopher Musa, ba za ta yi kowane irin nau’in rashin ɗa’a ga kundin tsarin mulki ba.

Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke kokawa game da rashin ba wa sojoji cikakkiyar kulawa, da cewa shaci-faɗi ne.

“Sojojin Najeriya sun gamsu, domin sun ma fi samun kulawa da jin daɗi a ƙarƙashin gwamnatocin dimokuraɗiyya,” a cewarsa.