Mazauna yankin Manga, wani gari da ke kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru wanda ’yan tawayen kasar na Ambazoniya suka kai wa hari a makon da ya gabata, sun ce an kashe musu mutum 13, ciki har da yara uku, sannan wasu 20 kuma sun bata.
Kakakin al’ummar yankin, Abubakar Manga, ne ya shaida wa wani kwamiti da gwamnatin Jihar ta kafa kan lamarin, lokacin da kwamitin ya ziyarcesu ranar Asabar.
Ya ce in ban da taimakon wani jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da ya kai musu dauki, da sai ’yan tawayen sun ga bayan ilahirin yankin.
Malam Abubakar ya kuma shaida wa kwamitin cewa ’yan tawayen kasar Kamarun na Ambazoniya sun tsallaka wani rafi ne sannan suka mamaye yankin nasu ta kan wasu tsaunuka da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Talatar da ta gabata.
Ya ce da farko sun fara kai hari ne gidan Dagacin garin inda suka kashe shi, kafin daga bisani su shiga harbin kan mai uwa da wabi har suka kashe mutum 13, ciki har da kananan yara guda uku.
Sai dai ya ce tallafin da jami’in NIS din ya kawo ne ta hanyar yin musatar wuta da su ne ya sa suka janye daga kan tsaunukan sannan suka gudu.
Abubakar ya kuma ce jami’in ya ceto wasu mutane da suka fada ruwa, inda ya ce har yanzu akwai mutum 20 da suka yi batan dabo, wadanda ya zuwa yanzu ake kyautata zaton sun mutu.
Sai dai ya ce rashin hanyoyin sadarwa ya dada ta’azzara matsalar, saboda babu damar su yi kiran gaggawa don a kawo musu dauki.
Da aka tambaye shi kan me ya sa suka kawo hari Najeriya, sai Abubakar ya ce, “Akwai ’yan uwanmu da suke a can Kamarun, wadanda yarenmu daya da su, sojojin Ambazoniyan suka kai musu hari, sai suka gudo garinmu, mu kuma muka ba su mafaka.”
Sun kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka ta girke musu jami’an tsaro a yankunan kan iyakokin domin tabbatar da tsaron kasa.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Takum, Mista Tikari, gargadin ’yan tawayen ya yi kan tsallakowa su kawo hari Najeriya, inda ya ce ba za su lamunci hakan ba a nan gaba.
Shi kuwa Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Danjuma Adamu, bayar da tabbacin girke jami’an tsaro ya yi a yankin, tare da kiran sojoji da su kafa sansaninsu a dukkan yankunan kan iyaka, kamar yadda yake a baya.