✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah

Barayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi.

Ya ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su a matsayin ’yan Najeriya masu son zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga makiyaya da su guji shiga gonaki, su kuma zauna lafiya da manoma domin hana rikice-rikice.

Usman ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da na jihohi bisa kafa ma’aikatar kiwo, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da makiyaya ke fuskanta.

Ya kuma yabawa gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris bisa ayyukan da suka inganta rayuwar al’ummar Fulani.