Akalla mutum 10 sun rasa rayukansu, wasu 20 kuma sun jikkata sakamakon harin bam a wani masallaci da ke yammacin birnin Kabul a lokacin da Musulmai ke tsaka da sallar Juma’a.
Mataimakin kakakin Ma’aikatar Cikin Gidan Afganistan, Besmullah Habib ya ce, an kai harin ne a masallacin Khalifa Aga Gul Jan a ranar Juma’a da misalin biyu na rana agogon kasar.
- Sai an kula da hakkin marayu Najeriya za ta zauna lafiya — Sheikh Bala Lau
- ’Yan bindiga sun saki hoton jaririyar da fasinjar jirgin kasan Abuja ta haifa a hannunsu
Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, harin ya auku ne a daidai lokacin da daruruwan Musulmai suka hadu a masallacin don sallatar Juma’a ta karshe a watan Ramadanan bana.
Haka nan, sun bayyana tsoronsu kan yiwuwar samun karin mutanen da za su rasu sakamako harin.
Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida da Taliban ta nada, Mohammad Nafi Takor, ya gaza yin karin haske kan lamarin, yayin da jami’an tsaron Taliban suka killace wurin.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin.
Wani ganau ya shaida wa Reuters cewa, wata fashewa mai karfi ta auku a masallacin a lokacin da masallata ke tsaka da ibada, fashewar ta kona kafafunsa da hannayensa.
Shi ma Mohammad Sabir, ya ce ya ga lokacin da aka kwashi mutane a cikin motocin daukar marasa lafiya bayan fashewar wani abu.
“Fashewar ta yi karfi sosai, har ma na yi tsammanin kunnuwana sun fashe,” inji shi.
Wata ma’aikaciyar jinya a yankin da ba ta yarda a ambaci sunanta ba, ta bayyana cewa sun karbi wasu da dama da suka jikkata a cikin mawuyacin hali sakamakon harin.