✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin kunar bakin wake ya kashe ’yan sanda 9 a Pakistan

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Wani dan kunar bakin wake ya kashe jami’an ’yan sanda 9 tare da raunata wasu 16 a harin da ya kai wa motarsu a Litinin din nan a Kudu maso Yammacin Pakistan.

Wani babban jami’in dan sanda, Abdul Hai Aamir ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a kusa da Dhadar, babban birnin gundumar Kachhi da ke da nisan kilomita 120 daga Balochistan, inda maharin ya daki bayan motar ’yan sandan da babur dinsa.

Hotunan da aka dauka bayan faruwar lamarin sun nuna yadda motar ta kife.

Babban jami’in ‘yan sandan gundumar Kachhi, Mehmood Notezai, ya shaida wa AFP cewa ‘yan sandan na kan hanyarsu ta dawowa daga wajen wani bikin baje-kolin shanu na tsawon mako guda da aka gudanar, inda suka samar da tsaro a wajen.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Yankin Balochistan na daga cikin yankunan da ke fama da barazanar tarwatsewa.

A watan da ya gabata sai da ’yan kunar bakin waken kungiyar TTP da ke biyayya ga Taliban suka kai harin da ya kashe mutane biyar a garin Karachi, baya ga harin bom da ya kashe sama da ’yan sanda 80 a masallaci a Arewacin Peshawar.