Mutum akalla 34 yanzu haka aka tabbatar sun mutu a sakamakon wani kazamin harin kunar bakin wake da wani ya kai kan masu ibada a masallaci a Pakistan.
Rundunar ’yan sandan kasar Pakistan ta sanar da hakan tana mai bayyana kazamin hari a matsayin ta’addanci.
- Wata Sabuwa: Dabdalar da ta wakana a Kannywood a makon jiya
- DSS ta cika hannu da ma’aikatan bankin da ke cuwa-cuwar sabbin kudade
Sanarwar rundunar ta kara da cewa, maharin ya tayar da abin fashewa ne a cikin wani masallaci da ke daf da harabar ginin ofishin ’yan sanda a kusa da birnin nan na Peshawar.
Kafofin watsa labarai da dama sun ruwaito cewa akasarin ginin masallacin ya rushe tare da danne masu ibada.
Akwai fargabar a samu karuwar asarar rayuka ta la’akari da munin harin da ya raunata wasu fiye da dari.
Akasarin wadanda suka mutun jami’an ’yan sanda ne, kawo yanzu babu kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai harin a kasar da ta jima tana fama da hare-hare masu nasaba da ta’addanci.