Gwamnan Jihar Neja, Anubakar Sani Bello ya yi kira ga al’ummar garin Kagara ta Karamar Hukumar Rafi a Jihar da su kwantar da hankalinsu saboda gwamnatinsa na yin duk abin da ya kamata domin kare rayuwa da kuma dukiyoyinsu.
Jawabin gwamnan na zuwa ne bayan wasu mahara sun kai wa al’ummar munana hare-hare da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma asarar dimbin dukiya.
A cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa, Misis Mary Berje, a ranar Alhamis, gwamna Sani ya ce babu wata gwamnati da ta san abin da take yi da za ta zuba idanu ana kashe mutanenta wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wasu ’yan bindiga sun yi wa garin na Kagara dirar mikiya inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi a garin ranar Laraba.
Gwamna Sani Bello ya tabbatar wa da mutanen Jihar cewa Gwamnatin Jihar da hadin gwiwar ta Tarayya da sauran jami’an tsaro domin magance matsalar tsaron da ke addabar jihar.
Ya kuma jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da addu’ar Allah Ya ba wadanda suka samu raunuka lafiya.
Gwamnan ya kuma nemi al’ummar jihar da su ci gaba da bayar da muhimman bayanan da za su taimaka wajen tarwatsa ayyukan bata-garin, yana ba su tabbacin samun kariya.