’Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun ba wa gwamnati wa’adin kwana bakwai ta biya musu bukatunsu.
’Yan bindigar sun ba da wa’adin ne a sabon bidiyo da suka saki mai mai dauke da wasu mutum shida daga cikin fasinjojin da ke hannunsu.
- Kisan Gillar IPOB: Dalilin da aka yi jana’izar Harira da ’ya’yanta a Anambra
- Yadda za a yi jana’izar matar da IPOB ta kashe tare da ’ya’yanta
’Yan bindigar sun zargi gwamnati da rashin gaskiya, kana suka ba ta wa’adin kwana biyar a kan su sako musu ’ya’yansu da suka ce ana tsare da su.
Da yake makagan, Mohammed Dehu, roko ya yi ga gwamnati ta saurari bukatun maharan don a kubutar da su.
Sabon bidiyon ya nuna fasinjojin a cikin halin galabaita, ciki har da wani dan kasar Pakistan.
An ji daya daga cikin fasinjojin na cewa, “Sunana Mohammed, ma’aikaci a nan Najeriya amma dan asalin Pakistan, an yi garkuwa da mu ne a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, Mu 62 a nan.”
Kazalika, wani daga cikinsu ya ce, “Yanayinmu a nan sam babu dadi, don haka nake rokon Gwamnatin Najeriya da ta Pakistan da kungiyoyin kasa da kasa da su taimaka a kubutar da mu.”
’Yan uwan fasinjojin sun sha yin magiya ga Gwamnatin Tarayya a kan ta taimaka ta ceto musu ’yan uwansu cikin koshin lafiya.
Idan dai ba a manta ba, ko a makon da ya gabata an ji Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, yana cewa, ana kan tattaunawa domin kubutar da fasinjojin da ke hannun ’yan bindigar.