’Yan bindiga sun sako kananan yara 11 daga cikin daliban da suka dauke a wata makarantar Islamiyya a garin Tegina ta Jihar Neja, saboda yaran sun kasa tafiya da sauri kamar sauran.
’Yan bindiga sun kutsa makarantar Islamiyyar Salihu Tanko a garin Tegina, suka bindige mutum daya, suka jikkata wani, sannan suka yi garkuwa da dalibai kimamin 200 da malamansu a ranar Lahadi.
“Kananan yara 11 da ba sa iya tafiya sosai daga cikin daliban makarantar Islamiyyar ne ’yan bindgar suka sako”, inji Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello.
Maharan sun kuma yi garkuwa da fasinjojin wata motar haya da ke kan hanyarta ta zuwa Minna, babban birnin Jihar a ranar Lahadin.
Gwamna Bello wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta tsakiya ya bayyana damuwa kan yawaitar ayyukan ’yan bindiga a kananan Hukumomin Rafi, Wushishi da Lavun na Jiharsa.
Sanarwar da ya fitar ta bayyana bacin ransa kan karuwar matsalar garkuwa da mutane, inda ya sake jaddada kiransa ga Gwamnatin Tarayya ta kawo wa jihar daukin gaggawa.
Ya ce, “Matsalar ta kai ‘intaha’ tamkar ana cikin halin yaki wanda ya kamata a tunkare shi nan take.”
Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar na kara bi gida-gida domin tabbatar da hakikanin yawan daliban da aka yi garkwa da su daga makarantar Islamiyyar.