Akalla mutum 45,000 ne suka rasa muhallansu a kasar Siriya bayan kazamin fadan da aka gwabza a tsakanin mayakan IS da dakarun Kurdawa na tsawon kwana uku, lokacin da Kungiyar IS ta kai hari kan gidan yarin Ghwayran da ke kasar.
Kazamin fadan da aka fafata a tsakanin bangarorin biyu ya yi sanadiyar hallaka fiye da mutum 140, ciki har da fararen hula.
- Ganduje ya nada Naburaska mai ba shi shawara a bangaren ‘farfaganda’
- Rikicin Rasha da Ukraine: Birtaniya za ta kara wa NATO sojoji
Mayakan IS sun kai harin ne da nufin kubutar da mambobinsu da ke tsare a gidan yarin mai matukar tsaro, lamarin da ya juye zuwa kazamin fada da ya hallaka rayukan mutane da dama.
Bayan kisan, mayakan sun yi awon gaba da kayayyakin aikin jami’an tsaron gidan yarin da wasu muhimman takardu da suke kunshe da wasu bayanai.