Likitoci a jihar Kogi sun karyata gwamnati Jihar da ta ce iyalan wata mara lafiyar da ba ta samu kulawa ba ne suka kai hari a Asibitin Gwamnati Tarayya (FMC).
Likitocin sun ce harin an kai shi ne dab da lokacin da suka gayyaci ‘yan jarida domin bayyana musu cewar suna da marasa lafiya a Asibitin da ke dauke da cutar COVID-19.
- Gwamna Akeredolu na Ondo ya kamu da COVID-19
- An sallami mutum na farko da ya kamu da coronavirus a Kogi
- Gwamnan Delta ya kamu da coronavirus
Takardar bayan taro da Shugaban Kungiyar Likitoci ta (NARD) Nnana Agwu, da na ma’aikatan lafiya na JOHESU Samuel Obajemu, da sauran shugabannin kungiyoyin lafiya a jihar suka fitar ta ce likitocin sun shiga yajin aiki har sai gwamnati ta samar musu kayan kariyar COVID-19 tare da yi wa ma’aikatan lafiya gwajin cutar.
Ma’aikatan lafiyan sun kuma ce rayuwarsu na cikin barazana sakamakon halin ko-in-kula da ake yi wa COVID-19 a Jihar.
Likitoci sun killace kansu saboda coronavirus
Wani daga cikin likitocin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wasu takwarorinsu sun killace kansu sakamakon mu’amalar da suka yi da marasa lafiyar da aka samu da cutar.
“Da yawanmu sun yi mu’ammala da masu cutar kafin a tafi da su Abuja. Abin takaici shi ne gwamnatin jiha ta ki daukar mataki”, inji shi.
Ya ce hakan shi ya sa suka nemi yin zanga-zangar lumana saboda Gwamnatin Tarayya ta san halin da suke ciki, amma ‘yan daba a cikin motoci suka shigo asibitin suna harbe-harbe a sama, suka kori ma’aikata tare da sace wayoyin hannu da kwamfutoci da na’urorin gwaji da wasu muhimman takardu.
Sai dai kuma kwamishinan watsa labarai na jihar, Kinsley Fanwo, a takardar da rabawa ‘yan jaridu ya ce, “Bincike ya nuna, dangin wata maras lafiyar da ba ta samu kulawa ba ne suka yi bore ga hukumar asibitin”.
Gwamnatin Kogi ta ki yarda akwai COVID-19 a jihar
Sai dai kuma har yanzu gwamnatin jihar ta ki yarda akwai cutar ta coronavirus a jihar duk da wasu mace-mace a jihar da ake zargin cutar ce ta yi sanadi.
Daga ciki akwai Babban Alkalin Jihar Nasiru Ajana da ya mutu a asibitin da ake kebe wadanda suka kamu da cutar a jihar.