✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bom ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin sojoji da al’ummar Kaduna

Al'umma sun ce harin bom ya kashe mutane 23 a masallaci, amma sojoji sun ce cibiyar ’yan ta'adda suka kai wa harin kai-tsaye

Al’ummar yankin Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna na zargin jiragen soji da jefa bom a kan fararen hula 23 a masallaci da kuma kasuwa.

Amma rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar wa Aminiya cewa jiragenta sun kai harin ne kai-tsaye a kan sansanin wani babban ɗan bindiga mai suna Kadaɗe Gurgu, wanda na hannun daman dan ta’adda Dogo Giɗe ne.

Amma mazauna ƙauyen Jika da Kolo da ke yankin Yadin Kidandan sun shaida wa Aminiya cewa daga cikin mutanen da harin jirgin sojin ya hallaka har da mutanen da ke zaune a kusa da masallacin.

Sun kamanta harin bom ɗin jirgin sojin na ranar Juma’a da wanda jiragen soja suka kai wa masu taron Maulidi suka kashe kimanin fararen hula 100, a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a watan Disamban 2023.

Sai dai kuma Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kafe a kan cewa ba ta kai harin na Yadin Kidandan ba, sai bayan da ta yi cikakken bincike ta kuma tabbatar da sahihancinsa game da taruwar ’yan ta’adda a wurin.

Rundunar ta tabbatar cewa ta kashe ’yan ta’adda da dama a harin, amma babu masallaci a wurin da jiragen suka kai harin.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilanmu cewa daga cikin waɗanda aka kashe a harin, har da ƙananan yara da manoma da suke kusa da masallacin a ranar.

Majiyoyi a yankin Kidandan sun tabbatar wa Aminiya cewa an yi jana’izar mutane 23 da gawarwakinsu suka rududduge a sakamakon harin bom da jiragen soji suka kai.

Wani shugaban al’umma a yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “gwarwaki 23 muka gano, cikinsu har da ƙananan yara, muka yi musu jana’iza.

“Hakika yankin Yadin Kidandan na da haɗari saboda yana ƙarƙashin ikon ’yan ta’adda.

“Amma akwai fararen hula da ba su ji ba, na su gani ba, da ke rayuwa a yankin saboda ba su da inda za su koma, irinsu ne wannan tsautsayi na ranar Juma’a ya shafa.

“Mun gano bayan harin cewa yawancin mutanen da ke masallacin sun mutu.”

“Wurin a cike yake da jama’a kuma akwai kasuwa a kusa da masallacin, su ma abin ya shafe su lokacin da aka kai harin da misalin ƙarfe 2 na rana,” in ji shi.

Wani mazaunin Kidandan wanda ya ce sunansa Malam, ya ce: “gaskiya ne sojoji sun kashe mutane da dama a ƙauyen Jika da Kolo ciki har da ’yan kauyenmu da suka je gona ko harkokin kasuwanci a kasu da masallacin.

“Akasarinsu manoma ne da kuma ƙananan yara da ke kusa da masallacin.”

Ya ce: “Da zuwan jirgin sai ya jefo wani abu, sai muka ji wata ƙara mai ƙarfi. Daga baya mutane suka je suka gano ’yan uwansu a cikin mamatan aka yi jana’izar”, a cewar Malam.

Labaran Hamidu, wanda ya halarci sallar jana’izar ya ce abin ya girgiza su, kuma ya tuna musu da abin da ya faru a Tudun Biri.

Don haka ya bukaci gwamnati ta gudanar da bincike ta ɗauki mataki a kan masu laifi.

Ya ce, “Yawancinmu muna zaune a nan ne saboda ba mu da wurin da za mu koma, kakanninmu ma a nan aka haife su.

“Idan da an yi bincike da an gano cewa ba a cikin kauyuka ’yan ta’adda suke zama ba, a cikin daji suke.”

Wani kansilama yankin, Abdullahi Isma’ilm ya tabbatar da harin, inda ga bayyana yankin a matsayin mai haɗari saboda ayyukan ’yan bindiga.

Cibiyar ’yan ta’adda muka kai wa hari —Sojoji

Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Gruf Kyaftin Kabiru Ali, ya shaida wa wakilinmu cewa cibiyar ’yan ta’adda kaɗai jiragen suka yi wa ruwan bama-bamai.

Gruf Kyaftin Ali ya tabbatar cewa babu masallaci a wurin har ya ba wakilanmu hotuna shaida da aka ɗauka kafin da kuma bayan harin.

Ya tabbatar da cewa jiragen ba su kai harin bom ɗin ba, sai da aka tabbatar da bayanan sirri da aka samu na taruwar ’yan ta’adda da makamansu da Dajin Yadi.

Hakazalika ya ce majiyoyi da dama da masu leƙen asiri a yankin sun tabbatar cewa harin ya tarwatsa cibiyar ’yan ta’addan gaba ɗaya kuma an kashe ’yan bindiga da dama.

Da aka tambaye shi game da harin masallacin da al’ummar sune zargi, sai ya ce, “a cikin hoton da ka gani, akwai inda ka ga masallaci a wurin?”

Ya ce: “Zuzzurfan bincike da bayanan da aka tattara sun tabbatar cewa akwai ’yan ta’adda da ababen hawansu a wurin.

“Bayanan sirri sun tabbatar cewa cibiyar ’yan bindigar da aka kai harin ta  ɗan ta’adda Kadaɗe Gurgu ne,  na hannun daman Dogo Gide.

“Runduanr ta samu tabbacin cewa Kadaɗe Gurgu ya ba da mafaka ga manyan ’yan ta’adda bayan sojoji a ragargaji su a jihohin Sakkwato da Zamfara.

“Bayanan da aka tattara sun nuna babu mazauna a wurin, amma da jiragen suna je sai ’yan bindiga suka fito daga cikin bishiyoyi suna tserewa daga yankin.

“Daga nan ne aka bude musu wuta ta sama aka hallaka su da maɓoyar tsasu,” in ji shi.

Gruf Kyaftin Ali ya ce za a ci gaba da kai irin waɗannan hare-hare har sai an ga bayan ’yan ta’adda a yankin Arewa ta Yamma da kuma Arewa da Tsakiya.

Gwamnatin Kaduna ta yi gum

Wakilinmu ya yi kokarin magana da Kwamishinan Tsaro na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, amma mai amsa kira ba ko rubutaccen saƙon da aka aika masa.