Hukumomi a kasar Pakistan sun ce akalla mutum hudu ne suka mutu lokacin da wani bam ya tashi a wani wajen taron siyasa a lardin Balochistan na kasar ranar Alhamis.
Bam din ya tashi ne a Quetta, wanda shi ne babban birnin lardin, a daidai lokacin da mambobin wata jam’iyyar ke kokarin bari wajen taron.
- Yadda za a shawo kan matsalar rashin Tsaro
- Dalilin da na gudu tun kafin Taliban ta kwace mulki – Tsohon Shugaban Afghanistan
Wani babban jami’in dan sanda a yankin, Fida Hassan Shah, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, “Akalla mambobin jam’iyyar hudu ne suka mutu, wasu 13 kuma suka jikkata a harin.
“Wani bam ne mai nauyin kilogiram 1.5 aka yi amfani da shi wajen kai harin,” inji Fida Hassan.
Javed Akhtar, wani jami’i a asibitin Sandeman da ke birnin na Quetta shi ma ya tabbatar da adadin wanda suka mutun ga AFP.
Kasar Pakistan dai na fama da ayyukan masu tayar da kayar baya daga kananan kungiyoyi daban-daban a kasar.
Ya zuwa yanzu dai, babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, wanda Babban Mai Shari’ar lardin ya bayyana a matsayin aikin ta’addanci.
Balochistan dai shi ne lardi mafi fama da talauci a Pakistan, duk kuwa da tarin albarkatun ma’adinan da yake da su. (AFP)