✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin bam a masallacin Juma’a ya hallaka sama da mutum 50 a Pakistan

Bam din ya fashe ne a masallacin ana tsaka da sallar Juma'a.

Wani bam ya fashe a cikin wani masallacin Juma’a da ke birnin Peshawar na kasar Pakistan, inda ya kashe akalla mutum 50 ya kuma raunata wasu da dama lokacin da suke tsaka da sallar Juma’a.

Rahotanni sun ce bam din ya fashe ne a masallacin Kucha Risaldar, mallakin ’yan Shi’a da ke birnin na Peshawar mai dimbin tarihi.

Hukumomin asibiti sun ce mutum 56 sun mutu, yayin da wasu 194 kuma suke cikin mawuyacin hali saboda raunukan da suka samu a harin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Shugaban ’Yan Sandan Jihar ta Peshawar, Muhammed Ejaz Khan, ya ce maharan sun kuma bude wa jami’ansu da ke wajen masallacin wuta.

Ya ce daya daga cikin maharan da dan sanda daya sun rasa ransu sakamakon wata musayar wuta, wani dan sandan kuma ya jikkata.

Muhammed Ejaz ya kuma ce daga nan ne daya daga cikin maharan ya kutsa kai cikin masallacin inda ya tayar da bam din.

Wani ganau mai suna Naeem, wanda gidansa ke dab da masallacin ya ce, “Da farko dai na ji karar bindiga kamar shida zuwa bakwai ne, sai na ga maharin ya shiga masallacin, daga nan sai ya tayar da bam din.

“Karar sai da ta bude kofar gidana, ni kuma na fadi a kasa. Lokacin da na shiga masallacin, hayaki da kura sun turnuke, inda na ga mutane a kwakkwance cikin jini,” inji Naeem.

Tuni dai Fira-Ministan kasar, Imran Khan ya yi Allah wadai da harin.

A ’yan watannin nan dai, kasar Pakistan ta fuskanci tashe-tashen hankula, inda aka kashe sojoji da dama a hare-haren da aka kai musu a ofisoshinsu da ke kan iyakar kasar da Pakistan.