✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Hare-Haren Jirage da Ambaliya Sun sa Boko Haram da ISWAP Gararamba

Luguden wutar jiragen yaki da kuma ambaliyar ruwan sama a Dajin Sambisa sun sa mayakan ISWAP da Boko Haram gararambar neman maboya.

Luguden wutar jiragen yaki da kuma ambaliyar ruwan sama a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno sun sa mayakan ISWAP da Boko Haram gararambar neman maboya.

Yanzu haka ’yan ta’ddan na neman mafaka a yankin Tafkin Chadi na Jamhuriyar Nijar, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa (AFP).

“Tserewar ’yan ta’addar ta karu a ’yan kwanakin sakamakon karuwar hare-haren jiragen yaki da ambaliyar ruwa da ta mamaye sansanoninsu,” in ji majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta.

Wata majiyar tsaro ta ce tun a watan Agusta ’yan Boko Haram ke tserewa daga Dajin Sambisa, sakamakon karuwan hare-haren bam a maboyarsu.

An kuma samu mamakon ruwan sama da ambaliya a kusan daukacin yankunan kasar.

Rahotanni sun nuna a ranar Litinin tawagar motoci sama da 50 dauke da mayakan Boko Haram da iyalansu sun bi ta wasu kauyukan jihohin Borno da Yobe, domin tserewa zuwa Nijar.

Wata majiya ta ce ana kyautata zaton mayakan masu biyayya ne ga shugaban Boko Haram, Bakura Buduma.

Ta ce motocin sun bi ta dajin Mafa zuwa cikin Jere da Koshobe kafin su tsallaka garuruwan Gajiram da Gasarwa, wadda ta hada Maiduguri da garin Monguno.

“(’Yan Boko Haram) sun tsallaka babban titin ne cikin jerin gwanon motoci 10 dauke da muggan makamai,” in ji Laminu Kontoma, wani mazaunin yankin.

“Bayan sun tsallaka babban titin ne motocin suka shiga dajin Gudumbali suka fito gefen Gaidam, suka tsallaka wani kogi zuwa gundumar Abadam da ke kan iyaka da Nijar,” in ji wani mazaunin garin Bunami Garga.

“Tabbas tawagar motocin Boko Haram na kan hanyar zuwa tsibiran da ke tafkin Chadi a yankin Bosso na Jamhuriyar Nijar inda kungiyar ke da sansanoni,” in ji wani masunci a yankin.

Shekara 13 ke nan da yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ke fama da hare-haren ta’addancin Boko Haram da ISWAP, wanda ya yi ajalin mutane sama da 40,000 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu.

Rikicin da ya faro daga Najeriya ya wasu zuwa kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da ke makwabtaka ita, inda kungiyar ke kamfa sansanoni a Yankin Tafkin Chadi da ke da iyaka da kasashen hudu.

Wadanda ke kan hanyar zuwa Nijar mayakan Boko Haram da wadanda aka yi garkuwa da su a wasu sassan Dajin Sambisa da suka rage a hannun kungiyar bayan ta sha ragargaza a hannun kishiyarta, kungiwar ISWAP ne suka tsere.

ISWAP ta balle daga Boko Haram a shekarar 2016, inda ta fi maida hankali wajen kai hare-hare kan sansanonin soji da kai wa sojoji kwanton bauna.

An kashe shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a watan Mayun 2021 a lokacin fafatawa da ISWAP, wanda kuma ya kwace mafi yawan yankunan kungiyar a Sambisa.

Wasu mayakan Boko Haram sun fice daga Sambisa zuwa dazuzzukan Arewa maso Yammacin kasar inda suka kulla kawance da wasu gungun masu aikata laifuka da ke da hannu wajen sace-sacen jama’a da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, kamar yadda wani rahoton hukumar leken asirin Najeriya ya nuna.