✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haramta yin acaba zai kawo karuwar ta’addanci —Masu babura

Matasa 66,000 za su shiga garari idan aka hana acaba a Gombe

Kungiyar ’Yan Achaba da Masu A Daidaita Sahu ta Kasa (NATCOMORAN) ta yi gargadi cewa shirin Gwamnatin Tarayya na haramta hawa babur zai haddasa karuwar matsalar rashin aiki da ta’addanci a Najeriya.

Kungiyar, Reshen Jihar Gombe, ta bayyana cewa haramta hawa babur a Jihar Gombe kadai zai raba mutum 66,000 da sana’arsu.

Shugaban NATCOMORAN Reshen Jihar Gombe, ta bakin mataimakinsa, Suleiman Sani, ya ce hana hawa babur zai mayar da mambobinsu marasa aikin yi, sannan talauci zai karu a kasa.

Da yake bayani kan kudurin da Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya gabatar, Suleiman Sani, ya ce, “Mutum 66,000 din nan fa masu rajista ne, akwai wadanda suke sana’ar acaaba amma ba su da rajista, ka ga ashe ba karamin bala’i ne zai faru ba.

“Mutum 66,000 da jiha daya idan aka hada jihohi 36 mutum nawa za a mayar marasa sana’a?

“Shin gwamnati za ta iya daukar dawainiyarsu dan kar ta’addanci ko sace-sace ya karu? Ba zai yiwu ba.”

Suleiman, ya kara da cewa baya ga masu sana’ar, akwai masu sayar da baburan da masu sayar da kayan gyara da masu faci da kanikawa, suma duk abun zai shafe su.

Ya ce idan gwamnati ta aiwatar da aniyar tata, to ba ta da hanyar samarwa wadannan mutane da iyalansu abinci.

“Zuwa yanzu babu wata hukuma da za ta iya daukar dubban mutanen nan, wanda hakan zai iya kara ta’azzara matsalar tsaro a fadin Najeriya,” in ji shi.

Wasu masu sana’ar acaba da muka zanta da su sun bayyana cewa hana hawa babur zai haifar da gagarumar matsalar rashin aikin yi da kuma karuwar matsalar tsaro.

Don haka suka kirayi gwamnati da ta janye wannan batu don gudun jefe kasar cikin mummunan yanayi.