✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu tsige Lamiɗon Adamawa ba —Majalisar

Majalisar ta ce sabuwar dokar masarautun ba ta taɓa matsayin Lamiɗon Adamawa na Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar ba

Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta ce har yanzu Lamido Adamawa ne shugaban majalisar sarakuna da hakiman jihar.

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar, Musa Mahmoud Kallamu, ya shaida wa taron ’yan jarida a ranar Juma’a cewa, dokar masarautun jihar ta tabbatar da Lamiɗon Adamawa a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan.

Kallamu ya bayyana cewa sashe na 17 na dokar ya kafa majalisar sarakunan jihar Adamawa, sashe na 18 ya zayyana mambobin majalisar, waɗanda suka haɗa da hakimai da hakimai masu daraja ta biyu da Babban Sakataren Ma’aikatar Masarautun Jihar da kuma Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi (ALGON).

Ya kuma jaddada cewa, wannan bai shafi matsayin Lamiɗon Adamawa na Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar ba.

Ya bayyana cewa shugancin majalisar masarautun shiyya-shiyya zai kasance na karba-karɓa ne, a karkashin kulawarLamido Adamawa wanda shugabansu na jihar.