✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Har yanzu dana yana hannun ’yan bindiga – Farfesa Ango Abdullahi

Sai dai ya ce ana sa ran kubutowar shi nan ba da jimawa ba

Mahaifin dan takarar kujerar Majalisar Wakilai a jam’iyyar PDP a mazabar Sabon Garin Zariya da ke Jihar Kaduna, Farfesa Ango Abdullahi, ya ce har yanzu dan nasa na hannun ’yan bindiga duk da lashen zaben fid da gwani.

Farfesa Ango, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Aminiya, lokacin da yake tsokaci kan nasarar da dan nasa, Sadiq Ango Abdullahi ya samu.

Sai dai ya ce suna sa ran dawowarsa gida nan ba da dadewa ba.

An dai sace Sadiq Ango ne tun lokacin da mahara suka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari, sannan suka sace mutane da dama.

Sadiq dai ya sami kuri’a 28 yayin da sauran ’yan takarar suka biyo baya.

Idan za a iya tunawa, tun a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2022 ’yan bindigar suka yi awon gaba da shi da wasu matafiya a jirgin kasa.

Tun a lokacin ba a sake jin duriyarsa ba a fagen siyasan ba.