✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu dai a kan Kwankwaso, Ganduje, APC da magoya baya

A makon da ya gabata a wannan fili na yi bayanin irin rigimar da ta kunno kai a cikin jam`iyyar APC, reshen Jihar Kano tsakanin…

A makon da ya gabata a wannan fili na yi bayanin irin rigimar da ta kunno kai a cikin jam`iyyar APC, reshen Jihar Kano tsakanin tsohon gwamnan jihar, yanzu kuma dan Majalisar Dattawa Sanata Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso da gwamnan jihar mai ci yanzu Dokta Abdullahi Umar Ganduje da jam`iyyarsu ta APC da magoya baya, tashin-tashinar da dama ta dade a kwance yanzu ta bayyana karara, tun bayan da mahaifiyar Gwamna Ganduje Hajiya Fatima ta rasu, shi kuma Sanata Kwankwaso ya je gaisuwar ta`aziyyar a rana ta uku. A yayin waccan ta`aziyyar an zargi Sanata Kwankwaso da daukar magoya bayansa da suka je kauyen na Ganduje, inda suka yi abubuwa na rashin da`a, kamar su zage-zage da sai sun CHANJA a shekarar 2019, da kuma daga hotunan Sanata Kwankwaso a zaman dan takarar neman shugabancin kasa a inuwar jam`iyyar APC, a zabubbukan 2019. Hakan ya kawo zuwa yanzu magoya bayan shugabannin biyu kowa ke goyon bayan nasa gwanin, alhali a gefe daya ana cewa za a shirya.
Bayan Gwamna Ganduje ya samu goyon bayan `yan Majalisar Dokokin jihar 34, daga cikin su 40, a wani kuduri da Majalisar ta zartas a cikin makon jiyan. Rikicin kuma ya zuwa yanzu ya ci kujerar mai tsawatarwar Majaisar, Alhaji Zubairu Mahmud Madobi dan Majalisa mai wakiltar mazabar Madobi a Majalisar Dokokin jihar, wadda ita ce mazabar Sanata Kwankwso, bisa ga irin dagewar da ya yi a wancan zama cewa, shi fa yana tare da tsohon Gwamna Kwankwaso. Sauran `yan Majalisar Dokokin jihar biyar da suka fito daga Mazabun Gwarzo da Tudun Wada da Dala da Rogo da Gwale, ana kyautata zaton su ma suna tare da Sanata Kwankwaso a wannan rikici. Kafin wannan matsayi na Majalisar Dokokin jihar `yan Majalisar sun kai wa Gwamna Ganduje ziyarar mubayi`a gidan gwamnatin jihar, inda suka neme shi da lallai sai ya ba da umurni ga dukkan magoya bayansa da su daina sa jar hula, bukatar da Gwamna Ganduje bai amince da ita ba. Ita ma kungiyar Shugabannin Zababbun kananan Hukumomin jihar ta ALGON, tuni ta kai ziyarar mubayi’a ga Gwamana Ganduje.
Shi kansa Gwamna Ganduje ya ci gaba da tereren kare kansa a kan wannan rikici, inda a lokacin da ya ke buda ci gaban aikin ginin hanyar Dakata zuwa Bela a cikin makon jiya aka ji shi yana cewa, gwamnatin da ya gada ta yi aiki a wani wuri, amma kuma a wani wuri da bai ambata ba aika-aika ta yi, aika-aikar da ya ce gwamnatinsa za ta bayyana su. Ya kuma fadi cewa, ya samu labarin cewa farkon wai abin da ya fara hada shi da Sanata Kwankwaso shi ne batun nade-naden da ya yi, akan wai bai nada mutanen Kwankwaso ba, Gwamna Ganduje yana mai jaddada cewa ai Sakataren gwamnatin jihar na Sanata Kwankwasa ne, haka kuma shi ma nasa ne, haka kuma labarin yake a kan Akantan-Janar, wanda shi ma ya gada daga Sanata Kwankwaso.
Ita kanta kungiyar tsofaffin Kansilolin jihar zuwa yanzu ta dare gida biyu, abin da har ya kai fagen aka dakatar da shugabanta bayan da ya bayyana goyon bayan kungiyar a kan tsohon gwamna, Sanata Kwankwaso. A can ma Majalisun Dokoki na kasa zuwa yanzu biyu daga cikin `yan Majalisar Dattawan Jihar Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da Sanata Barau Jibrin da wasu `yan Majalisar Wakilai 18, daga cikin 24, na jihar bayan wani taro da suka yi da Gwamna Ganduje a Abuja a karshen makon jiya sun jaddada cikakken goyon bayansu ga Gwamna Ganduje da gwamnatinsa, tare da neman magoya bayansu da sauran al`ummar jihar da su ci gaba da ba da hadin kai da goyan baya ga Gwamna Ganduje da gwamnatinsa, ta yadda zai ci gaba da samun sukunin gudanar da ayyukan ci gaba ga mutanen jihar baki daya.
Ko da a karshen makon jiya, sai da Rudunar `yan sandar jihar ta hannun Kakakinta DSP Magaji Musa Majiya, ta bayar da wata kakkausar sanarwa ta kafofin yada labarai, inda ta ce ta haramta wa wasu dubban`yan jam`iyyar APC da ta ce za su fito daga dukkan rassan kananan hukumomin jihar 44, yin wani gangami da jerin gwanon a Kano a ranar Lahadin da ta gabata, da aniyar su nuna goyon bayansu akan nasu gwanin (da ake kyautata zaton magoya bayan Sanata Kwankwaso ne) da su kuka da kansu, har sanarwar ta ce tuni rundunar ta yi nasarar cafke wasu daga cikin shugabannin da ake zargin sun shirya wancan gangami.
A can Abuja babban birnin tarayya inda Gwamna Ganduje yake saduwa da dukkan wadanda yake jin sun isa a fagen siyasar ta Jihar Kanon, an ruwaito shi yana fada wa manema labarai a fadar shugaban kasa, bayan ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa shi da Sanata Kwankwaso `yan uwan juna ne kuma abokai ne na siyasa, sabanin da ya shiga tsakaninsu na siyasa, yanzu kuma an dukufa wajen ganin an shawo kansa. Maganar da ake cewa wasu gwamnonin jihohi,  musamman na shiyyar Arewa maso Yamma (shiyyar da dukkan gwamnoninta na jam`iyyar APC ne ta kuma hada da Jihar Kano), da ita kanta uwar jam`iyyar APC ta kasa baki daya da fadar shugaban kasa zuwa yanzu duk sun dukufa wajen ganin sun gano bakin zaren wannan rikici.
Amma abin tambaya a nan, shi ne, ko tsoma bakin da uwar jam`iyyar APC da fadar shugaban kasa da sauran masu fada a ji na wajen Jihar Kanon, za ta iya kawo karshen wannan rikici, ko hayaniyar magoya bayan shugabannin biyu (`yan siyasar Jihar Kano), ita ma, za ta iya kawo karshen wannan dambarwa mai cike da tarihin cewa ba a Jihar Kano aka fara irinta ba, a cikin tarihin siyasar wannan jamhuriya, mai shekaru kusan 17? A tawa fahimtar ba za su iya ba, domin dukkansu kasuwar bukata ta hada su, ba akidar ci gaban jama`arsu ba, dadin-dadawa, ba jihar da aka taba samun sasanta irin wannan rikici ya zuwa yanzu, sai ma fadaduwarsa.
Don haka nike da ra`ayin kamata ya yi dukkan masu ruwa da tsaki na Jihar Kano, a nan ina nufin bangarorin nan uku na masu tafiyar da rayuwar kowace al`umma a ko ina, wato Sarakuna da Attajirai da Malaman addini, su ya kamata a jihar su shige gaba su gano bakin zaren dinke wannan fitina da ta kunno kai a Jihar Kano. Na nemi shigowar wadannan bangarori ne saboda matsayin da AllahYa ba su a cikinn al`umma, ta yadda a yau ba sai gobe ba, ba wani mai neman wani mukami, walau na a zabe shi ko a nada shi, ba tare da ya nemi hadin kai da gudummuwar wadannan bangarori ba. Su kuma shugabannin da suke tsakiyar rikicin da su fara sanya wa bakunansu linzami, dakatar da shugaban jam`iyyar APC na jiha da Sakataren tsare-tsare da aka yi a soke shi.
Ina ganin kuma yanzu ya kamata wadannan shugabannin al`umma su sa baki, domin idan wasu sun manta da irin rigingimun tashe-tashen hankulan siyasa da suka rinka haddasa gaba da kiyayya a tsakanin al`uma a jamhuriya ta farko ba, to bai kamata su manta da irin kashe-kashe da kone-kone da aka yi fama da su a jamhuriya ta biyu ba, a cikin rikicin bangarorin santsi da tabo, bangarori biyun da yanzu suke tsakiyar wannan rikici na APC. Allah Ya ba su ikon su motsa don ceton al`ummarsu da ma sauran al`ummar kasa baki daya.