Gwamnatin jihar Zamfara ta ce har yanzu akwai makarantun sakandare akalla guda 75 da suka shafe kusan shekara daya a rufe saboda matsalar tsaro.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Alhaji Kabiru Attahiru ne ya sanar da hakan a Gusau, babban birnin jihar ranar Asabar.
- Minista ya bukaci a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna nan da wata 4
- Liverpool ta kafa tarihin cin kwallaye 9 a wasa daya na Firimiyar Ingila
Yana jawabi ne yayin wani taron kwana biyu kan Manufar Ilimin ’Ya’ya Mata ta Kasa (NPGE) da aka gudanar a jihar.
Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Jihar (SUBEB) tare da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ne suka shirya taron.
Babban Sakataren ya lura cewa galibin makarantun da lamarin ya shafa na ’yan mata ne wadanda aka rufe tun a watan Satumban bara, bayan hare-hare har guda biyu da aka kai wa makarantun ’yan matan a jihar.
Sai dai ya ce gwamnatin jihar na ta aiki ba dare ba rana wajen ganin ta sake bude makarantun da aka rufe kusan shekara guda bayan barazanar ’yan ta’adda.
Gwamnatin jihar dai ta ba da umarnin rufe ilahirin makarantun jihar ne bayan sace dalibai 75 a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Kaya a karamar hukumar Maradun ta jihar.
(NAN)