Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan hanyoyin tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa daga inda muka a tsaya makon jiya. Da fatar Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da shi, amin.
1. Alayyaho na dauke da sinadarin magnesium wanda ke taimakawa wajen bayar da lafiyayyiyar iska ga jijiyoyin al’aura, kuma yana saukar da natsuwa ga mata, musamman lokacin ibadar aure. Haka alayyaho, kabeji da ganyayyaki ire-irensu na dauke da sinadarin indole-3 wanda ke rage yawan sinadarin oestrogen ga maza don haka sai testosteron ya samu karuwa, kuma suna kara yawan oestrogen ga mata.
2. Ayaba tana da yalwar sinadarin potassium da kuma bitamin B mai rassa da kuma sinadarin bromelain wadanda duk suna taimakawa wajen inganta lafiyar ma’akatar sha’awa da kara mata mai.
3. Baure yana cike da sinadaran amino acid wanda ke da alfanu wajen kara motsuwar sha’awa da kara mata karfi ga maza da mata.
4. Tafarnuwa tana dauke da sinadarin Allicin wanda ke taimakawa wajen malalar jini ga jijiyoyin al’aura, ta fi alfanu in aka hadiye ta danyarta, amma sai a san lokaci mafi dacewa na cin ta domin tana sa warin jiki da na baki, in mutum na warin tafarnuwa ko albasa, Mala’ikun rahama ba sa kusantarsa.
5. Alkama, in aka barza ta da kwansonta, aka yi fate ko kununta, ita ma tana kara karfin sha’awa, domin tana dauke da sinadarin L-arginine wanda ke zaburar da samar da sinadarin Nitric Odide wanda ke kula da zagayawar jini cikin jiki kuma yana sa jijiyoyin ibadar aure su bude su cika da jini sosai, wannan yana tabbatar da ingancin ibadar auren. Yazawa ma tana dauke da wannan sinadari mai alfanu.
6. Hatsi irin su masara, gero, dawa da sauransu in aka sarrafa su da kwansonsu, suna kunshe da sinadaran kara lafiyar sha’awa da ma lafiyar jiki duka. Don haka tuwon datsa ya fi tuwon surfaffiyar masara kara lafiya da inganta sha’awa, haka ma shinkafa ’yar gida ta hausa ta fi shinkafar bature ko shinkafar tuwo, domin tana dauke da sinadarin zinc, daya daga cikin sinadarai masu alfanu ga ma’aikatar sha’awa.
7. Barkono na dauke da sinadarin capsaicin wanda ke dumama jini don haka sai ya rika malala cikin jini. Haka kuma wannan sinadari na sa kwakwalwa ta saki sinadaran nishadi (endophins) cikin jini.
8. Zogale, binciken kimiyya ya tabbatar babu wani abinci da ke inganta lafiyar jikin dan Adam da bayar da waraka ga cututtuka daban-daban irin zogale, akwai matukar mamaki ga irin sinadaran karin lafiya da kuzarin da ke tattare da wannan ganye wanda zano su a nan zai dauki lokaci, don haka sai dai in ce da ma’aurata a durfafi cin zogale ka’in-da-na’in don samun lafiyayyar sha’awa, lafiyayyen jiki da lafiyayyen kuzari. Uwargida ta busar da danyen zogale, ta daka ta tankade sai ta rika barbada shi ga duk abinci har da na yara. Ana iya gauraya shi da zuma a sha, ko da madara, koko, nono da kowane irin abinci. Sannan a nemi man sa a rika amfani da shi daidai bukata. Don karin karfin kuzari da motsuwar sha’awa kuwa, uwargida sai ta samu barankacen ’ya’yan zogalen hade da furensa, sai ta dan yi farfesunsu sama-sama, kada su sha wuta sosai, sai ku ci tare da maigida, tare da shanye romon duka.
Sauran nau’ukan abincin masu kara sha’awa sun hada da citta; zuma; madara; dabino; aya; karas da duk kayan marmari da ganyayyaki.
Sai mako na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.